Connect with us

Uncategorized

An Shirya Walimar Karrama Farfesa Sa’adiya Bayan Nasarar ’Yan Najeriya A Gasar Alƙur’ani

Published

on

IMG 20260907 WA0037

Ƙungiyoyin addinin Musulunci a Jihar Sokoto sun shirya wata gagarumar walima domin karrama Farfesa Sa’adiya Omar OON, bayan nasarar da wakilan Najeriya suka samu a gasar Musabakar Alƙur’ani ta duniya da aka gudanar a Masarautar Saudiyya.

Ƙungiyar FOMWAN ta Jihar Sokoto ce ta shirya walimar, wadda ta samu halartar malamai, shugabannin ƙungiyoyin addini, ’yan uwa da abokan arziki, da wakilin Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, tare da sauran manyan baki.

Mun Ba Wa Ministan Tsaro kwana 7 Ya Janye Kalamansa Kan Mahaifinmu Ko Mu Kai Kararsa Kotu  —Iyalan El-Rufai

Farfesa Sa’adiya Omar OON ita ce Shugabar Kwamitin Amintattu na Musabakar Alƙur’ani ta Ƙasa, wadda ake gudanar da ita ƙarƙashin Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto. Ta ce nasarar da ’yan Najeriya suka samu a gasar ta nuna irin ƙwarewar da matasan ƙasar ke da ita a fagen karatun Alƙur’ani.

Najeriya ta samu wakilci daga jihohi daban-daban, ciki har da Kano, Gombe, Taraba da Zamfara. Daga cikin waɗanda suka yi fice a gasar akwai Maryam Dan Azumi Ibrahim Gwana, Hafsat Muhammad da Abdulmalik Inuwa, waɗanda suka wakilci Najeriya tare da sauran mahalarta.

Masu ruwa da tsaki a harkar addini sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da su ƙara ba masu karatun Alƙur’ani tallafi tare da karrama waɗanda suka samu nasara. Sun ce hakan zai ƙarfafa matasa su rungumi karatun Alƙur’ani tare da wakiltar Najeriya a manyan gasannin duniya.

Advertisement

Bayan walimar, Farfesa Sa’adiya Omar ta halarci shirye-shiryen tattaunawa da kafafen yaɗa labarai, inda aka tattauna kan nasarar ’yan Najeriya, muhimmancin Musabakar Alƙur’ani da kuma hanyoyin da za a bi wajen bunƙasa harkar karatun Alƙur’ani a Najeriya.

 

Rahoto: Mukhtar A. Haliru Tambuwal, Sokoto

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending