Uncategorized
CS-CRIN Ta Buƙaci ’Yan Jarida Su Jagoranci Yaƙi da Safarar Mutane
Ƙungiyar Civil Society Organisation for Conflict Resolution in Nigeria (CS-CRIN) ta buƙaci ’yan jarida su taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da safarar mutane, ƙaura ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifukan ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka a Najeriya.
Ƙungiyar ta kuma sanar da shirin kafa Journalists Against Transnational Organised Crime (JATOC), wata ƙungiyar musamman da za ta haɗa ’yan jarida domin gudanar da rahotannin bincike da wayar da kan jama’a kan waɗannan matsaloli.
Gwamnatin Kano Za Ta Takaita Zirga-zirgar Manyan Motoci Da Rana
Babban Daraktan CS-CRIN, Barrister Adeniyi Aremu, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da manema labarai da aka gudanar a Kano domin bayyana shirin ƙungiyar na “Strengthening Community Resilience and Institutional Capacity to Address Human Trafficking in Kano State, Nigeria.”
Gwamnatin Kano Za Ta Takaita Zirga-zirgar Manyan Motoci Da Rana
Shirin da Global Initiative ta ɗauki nauyinsa ƙarƙashin Resilience Fund, na da nufin ƙarfafa al’umma da hukumomi wajen dakile safarar mutane, kare waɗanda abin ya shafa da kuma inganta hanyoyin magance matsalar
Aremu ya ce za a fara kafa JATOC a Kano kafin a faɗaɗa ta zuwa sauran jihohin ƙasar.
Ya ce an riga an kafa kwamiti mai mutum biyar da zai jagoranci kafa da bunƙasa ƙungiyar.
A cewarsa, JATOC za ta samar da wata kafa da ’yan jarida za su haɗa kai, musayar bayanai da ƙarfafa aikin jarida mai zurfi domin tona asirin ƙungiyoyin da ke safarar mutane da sauran masu aikata manyan laifuka.
“’Yan jarida suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tona musabbabin safarar mutane, wayar da kan jama’a kan illolinta da kuma ƙalubalantar abubuwan da ke ƙarfafa ƙaura ba bisa ƙa’ida ba da cin zarafin mutane,” in ji shi.
Aremu ya ce kafafen yaɗa labarai na da babban tasiri wajen tsara ra’ayin jama’a, saboda haka za su iya taimakawa wajen dakile safarar mutane ta hanyar faɗakar da al’umma, yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya da kuma sanya hukumomi ɗaukar alhaki.b
Ya bayyana Kano a matsayin jihar farko a Arewacin Najeriya da CS-CRIN ta fara aiwatar da shirin, yana mai cewa daga nan za a faɗaɗa shi zuwa wasu jihohi.
Ya ce Kano na daga cikin muhimman wuraren da ake amfani da su wajen safarar mutane zuwa wasu sassan ƙasar da ƙasashen waje, lamarin da ya ce na buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin farar hula, al’umma da kafafen yaɗa labarai.
Aremu ya kuma buƙaci ’yan jarida su daina takaita rahotanninsu kan bayar da labarin abubuwan da suka faru kawai, inda ya ce ya kamata su gudanar da bincike kan abubuwan da ke haddasa safarar mutane da ƙaura ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ambaci ƙananan hukumomin Kumbotso da Ungogo a matsayin wasu daga cikin wuraren da ake ganin suna fuskantar matsalar, yana mai buƙatar ’yan jarida su binciki musabbabin lamarin.
“Ku taimaka mana wajen gano abubuwan da ke sa mutane su shiga safarar mutane da kuma dalilan da ke sa mutane yin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba a wannan yanki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa CS-CRIN na aiki tare da International Organization for Migration (IOM) wajen ƙoƙarin magance matsalar.
Aremu ya ce bayanan da ake da su sun nuna cewa cikin kimanin mutum 9,000 da suka dawo Najeriya daga ƙasashen waje cikin shekaru uku da suka gabata, kusan 5,000 daga cikinsu ’yan Kano ne.
Ya bayyana adadin a matsayin abin damuwa da ya kamata ya jawo hankalin hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce yawancin waɗanda suka dawo suna zaune ne a Kumbotso, Ungogo da wasu sassan jihar.
Babban Daraktan ya kuma jaddada muhimmancin yin rahoto cikin ƙa’ida da mutunta haƙƙin waɗanda aka yi safarar su.
Ya ce CS-CRIN za ta horas da ’yan jarida kan kalmomin da suka dace wajen bayar da rahoton safarar mutane, musamman yadda za a kare mutunci, sirri da haƙƙin waɗanda abin ya shafa.
Baya ga shirin JATOC, Aremu ya ce ƙungiyar za ta horas da kusan masu ba da shawarar shari’a 40 na al’umma, waɗanda za su taimaka wajen gano lamuran safarar mutane, ba da taimakon farko da kuma tura waɗanda abin ya shafa zuwa hukumomin da suka dace.
Ya kuma bayyana shirin horas da kusan ƙungiyoyin farar hula 150, ciki har da ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai.
A cewarsa, kafa JATOC zai ƙara ƙarfafa yaƙin da ake yi da safarar mutane ta hanyar samar da ƙungiyar ’yan jarida da za ta ci gaba da jan hankalin jama’a kan matsalar.
Shirin na da nufin sauya rawar kafafen yaɗa labarai daga bayar da rahoton safarar mutane kawai zuwa zama abokan haɗin gwiwa wajen rigakafi, bincike, wayar da kan jama’a, kare waɗanda abin ya shafa da kuma sanya hukumomi ɗaukar alhaki.
CS-CRIN ta ce faɗaɗa JATOC zuwa sauran sassan ƙasar zai taimaka wajen haɗa kan ’yan jarida wajen tona asirin ƙungiyoyin masu safarar mutane, kare muryoyin waɗanda suka tsira da kuma ƙara matsa wa hukumomi lamba su ɗauki matakan da suka dace.
Sabon bayanin da aka gabatar a Kano ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin CS-CRIN, NAPTIP, ’yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki wajen ƙarfafa yaƙi da safarar mutane.
-
News6 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News4 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
