News
Gwamnatin Kano Za Ta Takaita Zirga-zirgar Manyan Motoci Da Rana
Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta takaita zirga-zirgar manyan motoci a cikin kwaryar birnin daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa dare, a wani mataki na rage cunkoson ababen hawa da inganta zirga-zirga.
Kwamishinan Sufuri na jihar, Haruna Isa Dederi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce an kammala shirye-shiryen fara aiwatar da sabon tsarin.
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
Ya ce matakin ya zama dole ne sakamakon ƙaruwa da yawan jama’a da kuma bunƙasar harkokin kasuwanci a Kano, wadda ke cikin manyan cibiyoyin kasuwanci na Arewacin Najeriya.
A cewar kwamishinan, tsarin wani ɓangare ne na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da wani kamfani mai zaman kansa domin inganta harkokin sufuri da zamanantar da tsarin kula da zirga-zirgar ababen hawa.
Dederi ya ce hanyoyin shiga birnin guda shida ne za su kasance ƙarƙashin sabon tsarin. Su ne Kano–Katsina, Kano–Zariya, Kano–Danbatta, Kano–Gwarzo, Kano–Wudil da Hadejia.
Ya bayyana cewa takaita zirga-zirgar manyan motocin zai taimaka wajen rage cunkoso a manyan hanyoyin shiga birnin, tare da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da harkokin kasuwanci.
Da yake nasa jawabin, Manajan Daraktan kamfanin da ke haɗin gwiwa da gwamnatin jihar, Kafilu Abdulkadir, ya ce irin wannan tsari da aka fara amfani da shi a Jihar Legas tun shekarar 2007 ya taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa.
Abdulkadir ya ce za a gina babbar tashar ajiye manyan motoci a Daka Tsalle, domin samar da wurin da motocin za su tsaya kafin su samu damar shiga birnin.
Ya ce sama da manyan motoci 3,000 ne ke shiga Kano a kullum, lamarin da ya ce ke taimakawa wajen ƙara cunkoso a manyan hanyoyin shiga birnin.
A cewarsa, tashar ajiye motocin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta zirga-zirga a birnin Kano.
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News4 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
