Connect with us

News

Bai Kamata A Kafurta Wanda Bai Zabi Muslim-Muslim Ba’ —Sheikh Daurawa

Published

on

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce bai kamata a kafirta mutum ko a yi masa kallon wanda ya fita daga Musulunci saboda kawai bai goyi bayan tsarin takarar Musulmi da Musulmi a siyasar Najeriya ba.

Daurawa ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da DW Hausa a birnin Bonn na Jamus, inda ya ce babu wata jam’iyyar siyasa a Najeriya da za a iya cewa ita ce jam’iyyar Musulunci.

Biyan Haƙƙoƙin Tsofaffin Kansiloli Ba Siyasa Ba Ne – Waiya

A cewarsa, ’yan kasa suna da ’yancin zabar dan takarar da suke ganin ya fi dacewa da su, kuma bai kamata bambancin ra’ayin siyasa ya zama dalilin raba kan al’umma ba.

Ya ce bai kamata a mayar da addinin dan takara a matsayin babban ma’aunin zabe ba, domin akwai wasu muhimman abubuwa kamar cancanta, amana da kuma yadda zai iya wakiltar muradun jama’a.

“Kasancewar mutum Musulmi ko Kirista kadai ba ya tabbatar da cewa zai iya gudanar da mulki yadda ya kamata,” in ji shi.

Advertisement

Malamin ya kara da cewa bambancin addini bai kamata ya zama abin da zai raba al’umma ko ya hana ’yan Najeriya yin siyasa bisa la’akari da maslahar jama’a ba.

Daurawa ya kuma yi gargadin cewa bai kamata a kafirta ko a yi wa mutumin da yake da ra’ayi daban kan tsarin Musulmi-Musulmi hukunci na addini ba.

Kalaman malamin sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a Najeriya kan rawar da addini ke takawa a siyasa, musamman batun tsarin takarar Musulmi da Musulmi ko Musulmi da Kirista a zabukan kasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending