Opinion
Alakar Gwamna Namadi Da Badaru Za Ta Dore A Bisa Fahimta, Ko Kuwa Siyasa Za Ta Haifar Da Sabani Tsakaninsu? —Adnan Mukhtar
DAGA ADNAN MUKHTAR
Wannan hikima daga bakin wani fitaccen ɗan kasuwa a Amurka, Ziad K. Abdelnour, na ɗauke da darasi mai zurfi da ya dace da abun da ke faruwa tsakanin Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa da tsohon Gwamna, kuma yanzu Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar.
A lokacin da Badaru ke kan karagar mulki tsakanin 2015 zuwa 2023, shi ne ya fara ba Umar Namadi mukami a gwamnati — tun daga kwamishina, zuwa mataimakin gwamna. Wannan gina alaka ce da ta buɗe masa hanya har ya zama gwamna bayan Badaru ya kammala wa’adinsa.
SERAP Ta Bukaci Tinubu Ya Hana Wike Rufe Ofisoshin Jakadanci 34 A Abuja
Sai dai kamar yadda siyasar Najeriya ke da tarihi, sau da dama dangantaka tsakanin shugaban da wanda ya gaje shi na fuskantar sauyi bayan sauyin mulki. Wannan na haifar da tambaya: Alakar Namadi da Badaru za ta dore a bisa fahimta, ko kuwa siyasa za ta haifar da sabani tsakaninsu?
A yayin zabukan fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Jigawa, Badaru bai fito fili ya goyi bayan wani ɗan takara ba. Wannan hali nasa ya sa wasu ke ganin cewa hakan ne ya bai wa Namadi damar samun nasara, kasancewar babu wani babban jigo da ya tsaya takara da goyon bayan Badaru kai tsaye.
Wasu kuma na ganin cewa hakan na nuna kishin jam’iyya da hangen nesa da ke tattare da Badaru, domin ya bar tsarin ya gudana cikin adalci ba tare da katsalandan ba.
Wannan dabi’ar tasa ta janyo sauƙin canjin mulki a Jigawa — wani abu da ba kasafai ake samu a siyasar Najeriya ba.
Sai dai, tarihi ya nuna cewa sau da dama, magaji kan rabu da wanda ya gaje shi bayan samun mulki. Misalin wannan yana akwai a Zamfara, inda Mahmud Aliyu Shinkafi ya gaji Yarima Sani, amma daga baya suka yi sabani, wanda ya haifar da faduwar Shinkafi a zaben 2011.
To a Jigawa fa? Ko za mu ga irin wannan sauyin? Ko kuwa Gwamna Namadi da Badaru za su ci gaba da tafiya tare cikin fahimta, mutunta juna da girmama amanar da ke tsakaninsu?
Abin lura shi ne: siyasa na da sauyin fuska. Amma mutunci da amana su ne ginshiƙai na kowane irin dangantaka mai ɗorewa — musamman a harkar shugabanci. Da zarar an rasa ɗaya daga cikinsu, to akwai yiyuwar rikici.
A halin yanzu, idon al’umma na kan Jigawa. Kowa na sa rai ya ga yadda alakar Gwamna Namadi da Minista Badaru za ta ci gaba: Shin za su tsare amana da girmamawa? Ko kuwa siyasa ce za ta raba su?
Lokaci ne zai bayar da amsa.
