Connect with us

Opinion

Shamsudeen Bala: Lokaci Ya Yi da Za a Daina Cin Zarafin Matasa Masu Hankali —Adnan Mukhtar

Published

on

FB IMG 1750724287673
Spread the love

A cikin jerin matasan da suka gaji tarbiyya da mutunci daga iyayensu, Shamsudeen Bala Mohammed na daga cikin waɗanda suka zamo abin alfahari ga iyaye da al’umma gaba ɗaya. Matashi ne mai sauƙin kai, mai son zaman lafiya da kishin jin ƙai da ci gaban al’umma.

Wannan makala ba wai domin girmamawa kadai nake rubuta ta ba, sai domin kare wannan matashi daga mummunan suka da wasu ke yi masa, musamman zarge-zargen da suka fito daga bakin Omoyele Sowore da wasu da ke kallo da bambancin siyasa.

Sanata Kawu Sumaila: Wakilin Talakawa Da Gaskiya — Adnan Mukhtar

Zargin da aka dora masa na cewa wai ya sa aka kama wani malamin jami’a, bai da tushe, balle makama. Duk wanda ya karanta yadda lamarin ya wakana zai gane cewa an bi ƙa’ida da doka a kai ƙarar malamin da ake zargi da bata suna da kazafi. A bisa wannan ne jami’an tsaro suka cafke shi tare da miƙa shi gaban kotu don ya kare kansa.

Shamsudeen, kodayake ɗan gwamna ne, yana da haƙƙin kare martabarsa kamar kowanne ɗan ƙasa. Babu inda kundin tsarin mulki ko koyarwar addini suka ce ɗan siyasa ko ɗan mai mulki ba zai nemi adalci ba idan an bata masa suna.

Wannan doka ce, kuma ita ce ginshikin zaman lafiya da tsarin adalci a kowanne al’umma.

Omoyele Sowore dai, wanda aka sani da jan hankali da kirkiro labarai marasa tushe ta kafar Sahara Reporters, yana daga cikin masu tsoma baki cikin lamarin da gangan, da nufin gurgunta sunan matashin saboda kasancewarsa ɗan gwamna da kuma niyyarsa ta shiga siyasa.

Wani abin damuwa shi ne yadda Sahara Reporters ke wallafa labarai ba tare da tantance gaskiyar lamarin ba, lamarin da ke kara tabarbarewar fahimtar jama’a da haddasa rikici cikin sauƙi.

Bai kamata a ce ana kazafin mutum ba saboda kawai yana da burin siyasa. Ba zama ɗan gwamna ya hana mutum kare mutuncinsa da martabarsa ba.

Duk wanda ya san wannan lamari da kyau, zai tuna cewa Shamsudeen tun da farko ya fice daga duk wata alaka da bidiyon da ake ambato, har ma ya bukaci masu yadawa da su daina yada shi, kamar yadda ya bayyana a wani rubutun Facebook.

Ya kamata a riƙa duban gaskiya da adalci kafin yanke hukunci, ba tare da la’akari da matsayin wanda ake magana a kansa ba. Musulunci ya koyar da adalci da gaskiya a duk lamura, kuma hakan ne zai ba mu damar gina ƙasa mai daidaito da cigaba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *