Tawagar kai ɗaukin gaugawa ta jami’an ’yan sandan jihar Zamfara da aka tura a ƙauyen Lilo da ke gundumar Wonaka a cikin ƙaramar hukumar Gusau sun samu nasarar kashe jagoran ’yan bindiga Alhaji Lawali Dandumbulu.
Jagoran wanda ke jan ragamar tawagar ɓarayin a yankin Lilo da ke da iyaka da ƙananan hukumomi gudu uku da ke jihar ta Zamfara.
Wani mutum ya kai gawar ƴar’uwarsa banki don nuna shaidar ta mutu
Daga cikin harin da ’yan bindigar suka kai a ƙauyen ya rutsa da shi ya tarwatsa maɓoyar tasu a lokacin.
Al’ummar yankin fiye da ƙauyuka 30 ne suka yi ƙaura domin fargabar yuwuwar harin ‘yan bindigar.
Jim kaɗan bayan janyewar jami’an tsaron wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana yadda artabun ya kasance.
Ya ce, ’yan bindigar sun kai hari a ƙauyen Lilo ne a kan babura 44, bayan janye jami’an tsaron inda suka kashe mutu ɗaya tare da raunata wani da harbin bindiga suka kuma yi garkuwa da wasu mutane 9.
Ya ƙara da cewa, kafin isowar jami’an tsaron ’yan sanda da aka turo ’yan bindigar sun kai hari a ƙauyen na Lilo a babura fiye da 40 inda suka yi awon gaba da dabbobi fiye da 1000, suka ɓalle shagunan ’yan kasuwa da rumbunan abincin mutanen gari duk suka kwashe zuwa maɓoyarta su.
“ ’Yan bindigar sun kai harin a ƙauyen da babura 44 awanni kaɗan da janyewar jami’an tsaro.
“Sun kashe mutu ɗaya, sun harbi ɗaya, sun kuma yi garkuwa da wasu mutane 9 duk a Lilo.
