News
Abin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
Aminu Abdullahi Ibrahim
Abin da ya faru a Kano ya zama dole ya bata ran duk wanda ke girmama mutunci, al’ada, da kuma mutuncin mata.
Lamarin ya wuce a kalle shi a siyasa, abin tayar da hankali ne game da yadda ‘yan siyasa ke amfani da mata musamman wadanda suka rasa tarbiya wajen cimma muradansu.
Abin takaici ne a kyale mata su cire wandunan da aka basu akan titi suna dagawa a cikin al’ummar da ke alfahari da kunya da addini da girmama manya.
Bai kamata ayi watsi da irin wannan alamari ba saboda yadda yake nuna ƙaruwar lalacewar tarbiya.
Yaushe ne zubar da mutuncin mata ya zama abin tallatawa a yaƙin neman zaɓe?
Wasu dauka suke yi muna kalubalantar abinda suka yi ne saboda wani dan siyasa amma ba haka bane domin su dama ‘yan siyasa sun saba cin mutuncin junan su.
Amma duk cikin ‘yan siyasar da kuka yi wannan shirmen saboda su babu wanda ya fito da ‘yarsa ko kanwarsa ko matarsa ta cire wando akan titi tana dagawa.
