Connect with us

News

Majalisar Dokokin Kano Ta Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA

Published

on

Majalisar Dokokin Kano Ta Ce Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Zaben Kananan Hukumomin Da Aka Shirya Yi

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da soke dokar da ta kafa Hukumar Tsarawa da Bunƙasa Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), bayan sabon ƙudirin dokar tsare-tsaren muhalli da kula da bunƙasa gine-gine ya tsallake karatu na uku a zaman Majalisar da aka gudanar ranar Talata.

Zaman ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, inda ‘yan majalisar suka amince da sabon tsarin da gwamnatin jihar ta gabatar domin sake fasalin yadda ake gudanar da harkokin tsara birane da kula da gine-gine.

Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan zaman, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Hon. Lawan Hussaini Dala, ya ce soke dokar KNUPDA zai bai wa gwamnatin jihar damar kafa sabbin hukumomin bunƙasa birane guda biyu da za su maye gurbin hukumar.

Ya bayyana cewa sabbin hukumomin za su karɓi dukkan ayyukan da KNUPDA ke gudanarwa a baya, kuma za su kasance ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Muhalli ta Jihar Kano domin ƙara inganta ayyukan tsara birane da kula da ci gaban gine-gine.

A cewarsa, sabon tsarin zai taimaka wajen magance take dokokin gine-gine, tabbatar da bin ƙa’idojin tsara muhalli, da kuma inganta tsarin bunƙasa birane a faɗin jihar.

Advertisement

Hon. Lawan Hussaini Dala ya ƙara da cewa Majalisar ta amince gwamnatin jihar ta kafa Kano Metropolitan Development Authority (KAMDA) da Kano Area Development Control Authority (KADKA), waɗanda za su maye gurbin KNUPDA wajen gudanar da ayyukan tsara da bunƙasa birane.

 

Solacebase

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending