Politics
Sanata Kawu Sumaila: Wakilin Talakawa Da Gaskiya — Adnan Mukhtar
A ranar Juma’a, 29 ga Yuni, 2025, daruruwan al’ummar Kano ta Kudu sun hallara a Otal ɗin Dutse Royal da ke kan titin Maiduguri Road a birnin Kano domin ganawa da Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, wakilinsu a Majalisar Dattawa.
Taron wanda ya kasance gajere ne, ya bai wa Sanatan damar gabatar da irin ci gaban da ya samu a shekaru biyu da ya shafe yana wakiltar yanki a majalisar dokoki ta ƙasa.
Kashi 33% Na ’Yan Najeriya Na Fama Da Hawan Jini Ba Tare Da Sani Ba — Gwamnatin Tarayya
A cewar Sanata Kawu, ayyukan da ya aiwatar sun ratsa dukkan ƙananan hukumomi 16 da ke cikin Kano ta Kudu.
AYYUKA MASU MA’ANA
Daga cikin muhimman abubuwan da Sanatan ya bayyana akwai kafa Makarantar Sakandare ta Sojojin Ruwa a Sumaila, wacce ita ce ta farko a Arewa, da kuma taimakonsa wajen bude Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a Rano da Cibiyar Lafiya ta Tarayya a Rano.
Bugu da ƙari, a Garko kadai, Sanata Kawu ya bayyana cewa ya tallafa wa matasa da dama wajen samun guraben aiki a Rundunar Sojin Najeriya da ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Ayyukansa sun kai har zuwa Gaya, Ajingi, Albasu, Rogo, Karaye, Wudil, Doguwa, Tudun Wada, Takai, Kibiya da Bunkure – inda ake ci gaba da ambaton ayyukan da suka shafi ilimi, kiwon lafiya da gina matasan yankin.
GUDUMMAWA GA ILIMI
Sanata Kawu, wanda shi ne wanda ya kafa Jami’ar Al-Istiqama ta Sumaila, ya bayyana cewa ya na daukar nauyin sama da ɗalibai 600 da ke karatu a jami’o’i da makarantun gaba da sakandare a sassa daban-daban na ƙasar.
Wannan ya kara tabbatar da yadda yake bai wa fannin ilimi muhimmanci a cikin ayyukansa na wakilci.
SAUYIN JAM’IYYA BAI HANA GOYON BAYAN JAMA’A BA
Ko da yake Sanatan ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, hakan bai rage masa farin jini a tsakanin al’ummarsa ba. A cewar wasu daga cikin mahalarta taron, “abin da ya fi muhimmanci shi ne aiki, ba jam’iyyar da mutum ke ciki ba.”
Sanata Kawu ya bayyana cewa yana ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare muradun jama’arsa a majalisa, tare da daukar matakai ta hanyar gabatar da kudurori da motsa muhimman batutuwada suka shafi yankin.
