Politics
PDP Ta Sake Mayar Da Samuel Anyanwu Matsayin Sakataren Ƙasa Na Jam’iyya
Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP), ta sake tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren Ƙasa na jam’iyyar, bisa hukuncin da shugabancin jam’iyyar ya yanke a wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja, ranar Laraba.
Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Ambasada Iliya Damagum, ne ya bayyana haka yayin taron, tare da rakiyar wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da sauransu.
Da Tinubu Ba Shugaban Ƙasa ba Ne, Da Yanzu Yana Titi Yana Zanga-Zanga – Ndume
Damagum ya bayyana cewa daukar wannan mataki na dawo da Anyanwu cikin kwamitin aiki na ƙasa (NWC) bai kasance mai sauƙi ba, inda ya ce an yi la’akari da abubuwa da dama kafin yanke hukuncin. Haka kuma ya bayyana cewa taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka shirya gudanarwa daga bisani an soke shi.
Wannan mataki ya zo ne bayan wata ganawa da aka yi tsakanin shugabannin PDP da Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Talata, inda aka tattauna kan batun shari’ar da ta shafi kujerar Sakataren Ƙasa.
Ko da yake babu wata sanarwa kai tsaye daga PDP ko INEC bayan ganawar, majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa INEC ta shawarci PDP da ta gaggauta bin hukuncin Kotun Koli, wanda ya tabbatar da cewa jam’iyyar na da hurumin yanke hukunci kan shugabanninta.
Bugu da ƙari, INEC ta sanar da PDP cewa ba za ta karɓi wata wasiƙa ko sanarwa daga jam’iyyar ba, sai idan Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa da Sakataren Ƙasa sun sanya hannu a kai, kamar yadda dokokin hukumar zaɓe suka tanada.
