Connect with us

Politics

Yan Adawa Dake Sukar Tinubu Ba Don Talakawa Suke Ba, Sai Don Fushin Rasa Mulki – Shehu Sani

Published

on

1750866528054

Tsohon Sanata kuma ɗan  gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam, Shehu Sani, ya ce yawan sukar da ‘yan adawa ke yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba wai saboda jin ƙuncin talakawa ba ne, illa fushin rasa mulki da burin siyasa da bai cika ba.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wani shiri da aka watsa a tashar Channels Television mai suna The Morning Brief a ranar Laraba.

Advertisement

Mun Karɓi Buƙatar Ƙirƙirar Sabbin Jam’iyyun Siyasa Guda 110  — INEC 

A cewarsa, mafi yawan waɗanda ke fitowa suna sukar gwamnatin Tinubu tsoffin ‘yan siyasa ne da suka fito daga tsarin da suke suka a yanzu.

“Idan kana da gungun mutane da suka fusata saboda rashin nasara ko kuma domin an ware su daga gwamnati, to wannan ba wai don ƙasa ko don jama’a ba ne, illa dai fushin da suke ji saboda an fice da su daga mulki,” in ji Shehu Sani.

Advertisement

Tsohon Sanatan na Kaduna ya ƙara da cewa babu wani bambanci na ra’ayi ko akida tsakanin ‘yan adawa da masu mulki, yana mai cewa duka sun fito daga rukuni ɗaya na manyan ‘yan siyasa masu burin iko da suna.

“Su da waɗanda ke mulki yanzu duk daga tsari guda suka fito. Dukkaninsu sun sha rike madafun iko a baya, kuma suna da irin tsarin siyasa ɗaya,” in ji shi.

Advertisement

Shehu Sani ya ce sai da mutane su fahimci cewa galibin sukar gwamnati da ake yi a halin yanzu ba wai yana fitowa ne daga damuwa da halin da talakawa ke ciki ba, illa wata hanya ce ta nuna bacin rai da ɓacin zuciyar rasa mulki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending