Politics
Kwankwaso Na Fakewa da Talakawa Domin Cimma Burinsa, – Adnan Mukhtar
Wani ɗan gwagwarmaya kuma masani a fagen siyasa, Comrade Adnan Mukhtar, ya bayyana cewa siyasar Najeriya ta fi karkata kan muradun kai na ‘yan siyasa, ba wai muradin talakawa ba kamar yadda ake ikirari.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Adnan ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na amfani da sunan talakawa ne kawai a matsayin garkuwa domin cimma muradin kansa na siyasa.
NAPTIP Na Neman Speed Darlington Ruwa a Jallo Kan Zargin Cin Zarafi A Intanet
“Kwankwaso ba ya adawa da Tinubu saboda cire tallafin fetur ko tsadar rayuwa da ke addabar mutane ba, illa kawai saboda yana kallon Tinubu a matsayin babban cikas ga burin siyasarsa,” in ji Adnan.
Ya ce siyasar Najeriya ta koma wata hanya ta son zuciya da kare muradin kansu na kai, inda ya yi zargin cewa Kwankwaso yana iya haɗa kai da Tinubu a kowane lokaci idan hakan zai amfani burin sa.
Adnan ya ƙara da cewa: “Idan har Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai zaɓi mataimaki daga Arewa a zaben 2027, akwai yiwuwar ya zaɓi Rabiu Musa Kwankwaso ko Sanata Barau Jibrin. Wannan shi ne yadda siyasar Najeriya ke tafiya yanzu.”
Ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan siyasa na amfani da kalmar “talaka” ne kawai domin jawo hankalin jama’a, amma a zahiri ba su da wata damuwa da jin daɗin rayuwar talakawa.
“A zahiri, siyasar Najeriya siyasar kai ne, ba siyasar talaka ba,” in ji shi.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
