News
NAPTIP Na Neman Speed Darlington Ruwa a Jallo Kan Zargin Cin Zarafi A Intanet
Hukumar Hana Fataucin Mutane da Kare Hakkin Su (NAPTIP) ta bayyana mawakin nan kuma mashahurin mai tasiri a kafafen sada zumunta, Darlington Okoye, wanda aka fi sani da Speed Darlington, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Hukumar na zargin Darlington da aikata laifuka masu nasaba da fyade, cin zarafi ta intanet da kuma tsangwama ga mutane a kafafen sada zumunta.
Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Instagram a ranar Juma’a.
NAPTIP ta ce: “WANDA AKE NEMA RUWA A JALLO: Darlington Okoye, wanda aka fi sani da Speed Darlington, ana neman sa dangane da laifukan fyade, cin zarafi da kuma tsangwama ta intanet.”
A watan Mayu, NAPTIP ta gayyaci Darlington domin ya amsa tambayoyi dangane da wani zargi akan hulɗar jima’i da wata yarinya mai shekara 15.
A wata wasika da Shugaban Sashen Yaki da Laifukan Intanet na hukumar, Ngamaraju Mangzha, ya sanya wa hannu a ranar 28 ga Mayu, an bukaci mawakin da ya bayyana a hedikwatar hukumar a Abuja a ranar 30 ga Mayu, karfe 9 na safe.
Sai dai daga baya hukumar ta ce ta karɓi martanin Darlington, inda ya nemi a dage masa ranar zuwa 26 ga Yuni, yana mai cewa yana da wasu muhimman al’amura da suka sha gabansa.
Amma NAPTIP ta sake aiko masa da wata wasika wadda Darakta na Sashen Fasahar Sadarwa da Yaki da Laifukan Intanet na hukumar, Hakeem Lawal, ya sanya wa hannu, inda ta bayyana cewa ba za ta bi jadawalin mawakin ba. Ta sake umartar shi da ya bayyana a ranar 2 ga Yuni, a hedikwatar hukumar.
Duk da haka, rahotanni sun nuna cewa Speed Darlington bai bayyana a ranar da aka bukace shi ba.
NAPTIP ta ce tana ci gaba da neman sa, kuma ta bukaci jama’a da duk wanda ke da wani bayani kan inda mawakin yake, su tuntubi hukumar domin daukar matakin da ya dace.
