News
Ganduje Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban APC Na Kasa
Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na dab da miƙa takardar murabus daga mukaminsa a ranar Juma’a, idan dai ba a samu sauyin matsaya daga manyan jagororin jam’iyyar ba.
Majiyoyin da suka tattauna da wakilin DAILY NIGERIAN sun ce ana shirin maye gurbinsa da mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, har zuwa lokacin babban taron jam’iyyar da za a gudanar a watan Disamba mai zuwa.
Tsofaffin Ƴan Sanda Za Su Gudanar Da Zanga-Zanga A Faɗin Najeriya
Wani babban jigo a jam’iyyar ya shaida cewa dalilin murabus ɗin Ganduje ba ya rasa nasaba da ƙara yawaitar matsin lamba daga shugabannin yankin Arewa ta Tsakiya, wadanda ke ci gaba da yin tir da yadda aka karɓe musu shugabancin jam’iyyar tun bayan murabus ɗin tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu.
Tun bayan nada Ganduje a matsayin shugaban APC a watan Agustan 2023, akwai takaddama mai tsanani daga shugabannin Arewa ta Tsakiya, waɗanda ke ci gaba da matsa lamba da bukatar a mayar musu da shugabancin jam’iyyar.
Majiyoyin sun ƙara da cewa, tsohon gwamnan jihar Kano ya yanke shawarar sauka daga mukamin domin bai wa jam’iyyar damar sake tsara kanta tare da ƙarfafa tubalinta gabanin zaɓen 2027.
Sai dai har yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga jam’iyyar APC da ta tabbatar ko ta musanta jita-jitar murabus ɗin Ganduje.
