Labarai
Tsofaffin Ƴan Sanda Za Su Gudanar Da Zanga-Zanga A Faɗin Najeriya

Ƙungiyar Tsofaffin Jami’an Ƴan Sanda ta Najeriya, reshen jihar Kaduna, ta sanar da shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan a ranar 21 ga watan Yuli, 2025, domin nuna rashin jin daɗinsu kan tsarin fansho na haɗin gwiwa (Contributory Pension Scheme) da aka saka su ciki.
Shugaban ƙungiyar, Mannir M. Zaria, tare da mataimakinsa, Danlami Maigamo, ne suka bayyana hakan a wani taron wata-wata da suka gudanar a Police Officers’ Mess da ke Kaduna.
Prof. Gwarzo Ya Bai Wa Cibiyar Koyar Da Harshen Faransanci Ta Alliance Francaise Ofishi A Kano
Tsofaffin jami’an sun ce tsarin fansho na haɗin gwiwa ya jefa su cikin ƙuncin rayuwa da talauci, yana kuma haddasa musu ƙalubale da suka haɗa da rashin kima a idon jama’a, matsin tattalin arziki da kuma yawaitar rasuwar tsoffin ma’aikatan da suka yi ritaya.
Ƙungiyar ta bayyana cewa zanga-zangar za ta kasance cikin lumana, kuma za a gudanar da ita a lokaci guda a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Sun tuna cewa a baya sun gudanar da irin wannan zanga-zanga tun daga 24 ga watan Fabrairu zuwa 3 ga watan Maris, 2025, a harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa. A lokacin ne suka miƙa ƙorafinsu ga manyan shugabannin kwamitocin Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai, da kuma Ofishin Daraktan Hukumar DSS.
Sai dai Ƙungiyar ta bayyana jin takaici kan yadda har yanzu Majalisar Dokoki ta kasa fitar da matsaya dangane da sakamakon sauraron ra’ayoyin jama’a da ta gudanar kan ƙudurin kafa Hukumar Fansho ta Ƴan Sanda tun a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2024.
Tsofaffin jami’an sun nesanta kansu daga kowace ƙungiyar da ke da niyyar tayar da hankula ko haifar da tashin hankali a lokacin zanga-zangar, suna mai jaddada cewa nasu ya kebanta da neman kare mutuncin su da jin daɗin rayuwar su.
Ƙungiyar ta dage cewa kafa cikakkiyar Hukumar Fansho ta Ƴan Sanda ce kawai mafita ga matsalolin da suke fama da su, wanda suka bayyana a matsayin zalunci da take hakkinsu a tsarin fansho na yanzu.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
