Politics
Zaben 2027: Ina Goyon Bayan Hadakar Jam’iyyun Adawa Don Tabbatar Da Shugabanci Nagari — Peter Obi
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, ya bayyana goyon bayansa ga yunƙurin da ake yi na haɗakar jam’iyyun adawa domin samar da shugabanci nagari a zaɓen 2027.
Peter Obi ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya ce yana tare da duk wata ƙungiya ko haɗaka da ke da nufin kawo canji mai amfani ga Najeriya.
Yin Taku 5,000 Sau Uku A Mako Na Rage Hadarin Kamuwa Da Cututtuka —Bincike
A cewarsa, Najeriya na bukatar sabuwar hanya ta shugabanci da za ta mayar da hankali kan inganta rayuwar talakawa, farfado da tattalin arziki da kuma magance matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar.
Obi ya bayyana cewa, haɗin kan jam’iyyun adawa ba alamar rauni ba ne, illa kuwa wata dama ce ta haɗa ƙarfi da ƙarfi don fuskantar kalubalen da ke gaban ƙasa.
”Ina tare da kowane yunƙuri da zai kai mu ga samun shugabanci nagari a 2027. Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu fahimci cewa Najeriya na bukatar shugabannin da suka damu da ci gaban al’umma, ba na kansu ba,” in ji shi.
Peter Obi ya kuma jaddada muhimmancin gaskiya da rikon amana a cikin wannan tafiya ta haɗakar adawa. Ya ce, rashin sadaukar da kai da son zuciya daga wasu shugabannin siyasa na iya zama babban cikas ga nasarar da ake fatan samu.
Ya ƙara da cewa: “Wannan lokaci ne na ceto Najeriya daga halin da take ciki, ba lokacin yin faɗa da juna ko nuna bambanci ba.”
Obi ya ce yana maraba da duk wani tsarin da zai bai wa ‘yan Najeriya damar samun shugabanci na gari a zaɓen 2027.
