News
Yin Taku 5,000 Sau Uku A Mako Na Rage Hadarin Kamuwa Da Cututtuka —Bincike
Wani sabon bincike da aka gudanar a Birtaniya ya nuna cewa yin taku 5,000 a kowanne lokaci sau uku a mako, na iya taimakawa matuka wajen kare mutum daga kamuwa da cututtuka masu tsanani.
Nazarin wanda aka gudanar tare da hadin gwiwar Kwalejin Nazarin Siyasa da Tattalin Arziki ta London (LSE) da wani kamfanin inshora na kasar, ya shafi sama da mutane miliyan daya daga kasashen Birtaniya da Afirka ta Kudu.
Gwamnatin Plateau Ta Tura Wakilai Zaria Don Jajantawa Kan Kisan Matafiya
Jaridar The Times ta ruwaito cewa, nazarin ya dauki tsawon shekaru goma ana bin diddigin halayen motsa jikin wadannan mutane, tare da duba yadda lafiyarsu ke tafiya.
Sakamakon nazarin ya nuna cewa, wadanda ba su cika motsa jiki ba, idan suka dage suna yin taku 5,000 a kowanne lokaci sau uku a mako, za su iya tsawaita rayuwarsu da tsawon shekaru biyu zuwa uku.
Binciken ya kara da cewa, motsa jiki na kowane minti yana da tasiri wajen rage hadarin kamuwa da cututtuka kamar ciwon zuciya, ciwon siga da cutar sankara.
A cewar masana, daga cikin wadanda suka fi yin motsa jiki akai-akai, musamman masu yin taku 10,000 a kowanne lokaci sau uku a mako, an samu raguwar hadarin kamuwa da wadannan cututtuka idan aka kwatanta da wadanda ke zaman kashe wando.
Binciken ya kuma bayyana cewa, ma wadanda ke fama da ciwon siga za su iya amfana daga irin wannan motsa jiki.
Misali, wani mutum mai shekaru 55 da ke fama da ciwon siga, idan ya dage yana yin taku 5,000 sau uku a mako, hadarin mutuwarsa zai iya raguwa da kashi 40 cikin dari idan aka kwatanta da takwarorinsa da ba su motsa jiki.
Wani bangare na binciken ya nuna cewa ko da wadanda ba su da koshin lafiya za su iya fara da taku 5,000 kafin daga bisani su karu da yawan tafiyar.
Madam Zhang Chuji, likita a Asibitin Tiantan na Beijing, ta ce ko da yake yin taku 10,000 a rana shi ne abin da aka fi bada shawara, amma yin taku 5,000 sau uku a mako ma yana da matukar amfani.
Ta ce, “Wadanda ba su saba da motsa jiki ba, za su iya fara da taku 5,000. Wannan zai rage hadarin cututtuka kuma ya inganta lafiyar jiki da kwakwalwa.”
Masana lafiyar jama’a na ci gaba da karfafa gwiwar mutane su rika yin motsa jiki domin kauce wa kamuwa da cututtuka da kuma tsawaita rayuwa.
