Connect with us

News

Gwamnatin Plateau Ta Tura Wakilai Zaria Don Jajantawa Kan Kisan Matafiya

Published

on

IMG 20250629 WA0011 1

Wakilan gwamnatin Jihar Plateau sun isa garin Zaria a Jihar Kaduna domin mika sakon ta’aziyya ga al’ummar da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon harin da aka kai matafiya ‘yan Zaria a Mangu, Plateau.

A ranar Asabar da ta gabata ne Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda gwamnatin Plateau ta gaza turo wakilai domin jajantawa tun bayan faruwar lamarin.

Advertisement

Mahara Sun Sace Hakimi A Kaduna

Sai dai a yau Lahadi, gwamnatin Plateau ta tura wata tawaga karkashin jagorancin Sarkin Wase, Alhaji Sambo Haruna Muhammadu, domin yin gaisuwar ta’aziyya ga Sarkin Zazzau da iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Da yake bayani a lokacin da suka isa Fadar Sarkin Zazzau, Sarkin Wase ya bayyana cewa sun jinkirta zuwan ne sakamakon dalilan tsaro, amma yanzu sun samu tabbacin cewa tafiyar ba za ta fuskanci matsala ba.

Advertisement

Mun so mu zo tun da farko, amma dalilan tsaro da kuma bukatar samun cikakken tabbaci ne ya sa muka jinkirta. Muna rokon afuwa a madadin gwamnatin Jihar Plateau,” in ji Sarkin Wase.

Ya ce akwai wata tawaga ta biyu wadda za ta sake zuwa domin jajantawa musamman ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Advertisement

A halin yanzu, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da kama mutane 22 da ake zargi da hannu a harin da ya yi sanadiyyar mutuwar matafiya 13 da suka fito daga Zaria zuwa Mangu domin halartar biki.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending