News
Farfesa Gwarzo ya taya Hadiza Ma’aji murnar kaiwa ga matakin Farfesa da Jami’ar ABU ta yi mata
Shugaban jami’o’in Maryam Abacha, MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya mika sakon taya murna ga Hadiza Usman Ma’aji bisa daukaka matsayinta zuwa matakin Farfesa a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) dake Zariya.
Zaben 2027: Ina Goyon Bayan Hadakar Jam’iyyun Adawa Don Tabbatar Da Shugabanci Nagari — Peter Obi
Jami’ar ta ɗaga matsayin Hadiza zuwa matakin Farfesa a fannin haɗa magunguna.
Sakon taya murna na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Adamu Gwarzo ya sanya wa hannu da kansa kuma aka raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Farfesa Gwarzo ya kuma yi amfani da wannan damar wajen karrama Farfesa Hadiza Usman Ma’aji a matsayin farfesa mace ta farko a fannin magunguna na Clinical Pharmacy a yankin Arewacin Najeriya.
“A matsayinki na mace ta farko a Arewacin Najeriya wacce ta kai matakin Farfesa a fannin magunguna na Clinical Pharmacy, Hadiza Usman Ma’aji kin cancanci yabo, girmamawa, murnar da alfahari da kaiwa ga irin wannan kololuwar mataki na karatu.
“A madadin hukumar gudanarwar rukunin jami’o’in MAAUN, ina taya ki murnar karin girma da majalisar Koli ta ABU ta tabbatar miki.
Farfesa Gwarzo ya kara da cewa Farfesa Hadiza, wacce ‘yar Arewa ce, amma ta ketara zuwa jami’ar Ibadan da Nsuka domin yin digirnta na biyu da na uku, kafin kaiwa ga wannan mataki.
A karshe ya yi mata fatan Alkhairi da kuma addu’ar Allah ya sanya Alkhairi a wannan mataki na karatu da takai a rayuwa.
