News
Kashi 33% Na ’Yan Najeriya Na Fama Da Hawan Jini Ba Tare Da Sani Ba — Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa fiye da kashi 33 cikin 100 na ’yan Najeriya — wato mutum ɗaya cikin uku — na fama da cutar hawan jini, cutar da ke kashe mutane a sannu ba tare da wata alama ba, sannan da dama daga cikinsu ba su da masaniyar suna dauke da ita.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara ta musamman kan harkokin lafiya, Dr. Salma Anas, a lokacin da take jawabi a taron shekara-shekara na 25 da ƙungiyar likitocin hawan jini ta ƙasa (Nigerian Hypertension Society) ta shirya a birnin Abuja.
Akwai Yiwuwar Kwankwaso Ya Zama Abokin Takarar Tinubu A 2027
Taken taron na bana shi ne: “Ƙara Ƙaimi Wajen Kula da Hawan Jini a Najeriya: Tsare-tsare, Tsarin Lafiya da Ayyuka.”
Matsanancin Halin Da Masu Cuta Ke Ciki
Dr. Anas — wadda Mista Umar Tanko ya wakilta — ta bayyana cewa “binciken lafiya ya tabbatar da cewa daga cikin kowane mutum uku a Najeriya, akwai wanda ke fama da hawan jini.”
Ta ƙara da cewa “abin damuwa shi ne, mafi yawansu ba su da masaniya game da wannan mummunar cuta da ke ci gaba da ta’azzara matsin rayuwa da yawan mace-mace a ƙasar.”
“Akwai babbar baraka tsakanin yawan waɗanda ke da cutar da kuma yawan waɗanda ke samun ingantacciyar kulawa ko magani,” in ji ta.
Dalilan Da Ke Haddasa Matsalar
Ta ce akwai dalilai da dama da ke hana yaduwar magani da kulawa, ciki har da tsadar magunguna, ƙarancin cibiyoyin lafiya da kuma rashin shirin gaggawa daga hukumomi wajen tallafa wa marasa lafiya.
Dr. Anas ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara ɗaukar matakan gyara, domin daƙile wannan barazana ga rayukan ’yan ƙasa, da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.
A cewarta, gwamnati na ƙoƙarin inganta tsarin kiwon lafiya, musamman wajen rage dogaro da magunguna daga ƙasashen waje, da kuma samar da su a cikin gida.
Kisan Mummuƙe Ne – Farfesa Isezuo
Shima a nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Likitocin Hawan Jini ta Najeriya, Farfesa Simon Isezuo, ya bayyana hawan jini a matsayin cuta mai kisan gilla, wadda ke ɗaukar rayukan mutane cikin sannu ba tare da wata alama ta gaggawa ba.
“Kasa da kashi 10 cikin 100 na waɗanda ke shan magani ne ke iya daidaita matsin lambar jininsu yadda ya kamata. Wannan ne ke haddasa bugun zuciya, gazawar koda da mutuwar ba-zata,” in ji shi.
Wayar da Kai da Canjin Hali Na Da Matuƙar Mahimmanci
Farfesa Isezuo ya bukaci ƙarin wayar da kai, da gudanar da bincike mai zurfi, da kuma fadakar da jama’a kan barazanar hawan jini da haɗarin amfani da gishiri fiye da kima.
Ya kuma shawarci jama’a da su rungumi motsa jiki kamar yawo da gudu, da rage nauyin jiki domin kariya daga kamuwa da cutar ko kuma daidaita ta.
