Connect with us

News

Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Satar Kayan Layin Dogo A Ilorin, Kano Da Gombe

Published

on

Rail tricks

Rundunar ‘yan sandan hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), ta ce ta kama wasu da ake zargi da satar kayan layin dogo a jihohin Kwara, Kano da Gombe.

Manajan Daraktan Hukumar, Dakta Kayode Opeifa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, a birnin Lagos.

Advertisement

Shamsudeen Bala: Lokaci Ya Yi da Za a Daina Cin Zarafin Matasa Masu Hankali —Adnan Mukhtar

Ya ce an kama waɗanda ake zargi da satar manyan farantan tayoyin jirgin ƙasa, takalman birki, karafa da sauran muhimman kayayyaki da ke cikin layin dogo a wasu sassa na ƙasar.

 

Advertisement

A cewarsa, a ranar 11 ga Yuni, wani ma’aikacin tashar jirgin ƙasa da ke Ilorin, Mista Adesina Fabumi, ya kai rahoton satar farantan tayar jirgi guda 56 da wasu kayayyaki, da aka kwashe a kusa da kauyen Idi-Ose, tsakanin kilomita 413 zuwa 414.

 

Advertisement

“Rundunar ta kama wani da ake zargi da laifin, mai suna Usman Bashir, a ranar 18 ga Yuni, kuma an same shi da kayayyakin layin dogo a hannunsa,” in ji Opeifa.

 

Advertisement

Ya kara da cewa Sufeta Oniwara Musa na ci gaba da gudanar da bincike domin kama sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.

 

Advertisement

A jihar Kano kuwa, rundunar ‘yan sanda ta ce ta kama wasu mutum hudu a ranar 15 ga Yuni, bayan samun rahoton barna da aka tafka a layin dogo da ke garin Zakirai, ƙaramar hukumar Gabasawa.

Opeifa ya ce an gurfanar da su a gaban kotu, inda suka amsa laifin da ake tuhumar su da shi, kuma kotu ta yanke musu hukunci.

Advertisement

Ya ce hukumar NRC za ta ci gaba da kare duk wata kadara da ta shafi layin dogo, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi ba zai guje wa hukunci ba.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending