News
Za a fara aikin layin dogo daga Kano zuwa Lagos da kuma Fatakwal zuwa Aba kafin Disamba – NRC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kamfanin jirgin kasa na Najeriya ya ce za a fara aikin layin dogo daga Kanozuwa Lagos da kuma Port-Harcourt zuwa Aba nan da Disamba 2023.
Fidel Okhiria, Manajan Darakta na Kamfanin Jiragen Kasa na Najeriya, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Malam Ibrahim Musa
Ya kara da cewa Bayan da ‘yan kwangilar suka ba da tabbacin, fasinjoji da jigilar kaya za su fara kan titin jirgin Kano zuwa Legas da kuma Fatakwal zuwa Aba,
Haka gwamnatin tarayya na kokarin tabbatar da tsaro a bangaren sufurin jiragen kasa a kasar nan
“A cikin watanni uku masu zuwa, za mu iya fara aiki a Kano zuwaLagos da kuma Fatakwal zuwa Aba. Don haka za mu iya tashi daga tashar jiragen ruwa,” inji shi.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa cewa fannin ya samu Naira miliyan 768.4 a farko na shekarar 2023 (Q1’23) daga Naira biliyan 1.15 a Q4’22, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS ta bayyana.
Wani labarin kuma Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Malam Ibrahim Musa
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro