Connect with us

News

Kungiyar Miyetti Allah na so a yi wa duka dabbobin kasar nan rigakafin cutar anthrax

Published

on

Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a ta yi kira ga gwamnatin kasar ta yi wa duka dabbobin kasar rigakafin cutar anthrax wadda aka samu barkewarta a Jihohin Neja da kuma Legas.

Advertisement

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa rigakafin ne kawai mafita ta magance wannan matsalar baki daya.

Za a fara aikin layin dogo daga Kano zuwa Lagos da kuma Fatakwal zuwa Aba kafin Disamba – NRC

“Duk da cewa a jihohi biyu kawai aka bayar da rahoton barkewar cutar, hakan ba yana nufin ba za ta iya watsuwa zuwa sauran jihohi ba.

Anthrax cuta ce da ke yaduwa tsakanin dabbobi da mutane kuma lamari ne da ya shafi tsaron kasa. Ganin yadda take bazuwa da jawo mace-mace, ya zama dole a magance ta cikin gaggawa,” in ji sanarwar.

Advertisement

Kungiyar ta ce Nijeriya na da sama da shanu miliyan 20 da tumaki da awaki miliyan 75 kuma ana shiga da wasu kasar daga makwabtan kasashe.

“Mambobinmu sun yi asarar sama da shanu miliyan uku a rikicin da ake yi da satar shanu a fadin jihohi, ba mu shirya yin wata asara ba,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta Miyetti Allah ta jinjina wa gwamnatin Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya kan sayo rigakafin anthrax da za a yi wa duka dabbobin da ke jihar inda ta bukaci sauran jihohi su yi koyi da ita.

Advertisement

Matakan kariya daga cutar anthrax

Cutar anthrax da ake samu daga cin naman dabbobi takan nuna alamu kamar ciwon ciki, amai, tashin zuciya, ciwon kai, da gudawa mai zuwa da jini.

Dr. Sule Ali Gabas, wani likita a Sagmediconsult and Diagnostic Services Ltd, a Accra, ya bayar da wasu shawarwarin da za su taimaka wajen kauce wa wannan cuta.

Advertisement

Nisanta mu’amala ko taba dabbobin da suka kamu

Kaurace wa nama ko nono ko duk wani abu da ya fito daga dabba mara lafiya

Daina shiga yankin da cutar ta bayyana har sai an shawo kanta

Advertisement

Garzayawa asibiti idan an fuksanci alamu ko barazanar cutar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *