Connect with us

News

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Malam Ibrahim Musa

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Malam Ibrahim Musa, wanda da farko take tsare da shi.

Advertisement

Ɗan uwan Editan, Abdullahi Usman ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ran Juma’a.

Nijeriya ta rasa damar karɓar baƙoncin gasar kofin Afrika na 2027

Jaridar Inda Ranka ta rawaito jami’an DSS sun tsare Ibrahim Musa a Babban Filin Jirgin Saman Aminu Kano da ke Kano da safiyar Larabar da ta gabata a lokacin da yake ƙoƙarin tafiya Umara a Saudiyya.

Bayanai sun ce an sako Editan a ranar Alhamis, kuma an maida masa dukkan takardunsa na tafiya.

Advertisement

Usman ya ce lafiya ƙalau Editan ya koma cikin ahalinsa da ‘yan da abokan arziki.

Wani labarin kuma Nijeriya ta rasa damar karɓar baƙoncin gasar kofin Afrika na 2027

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Advertisement

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *