News
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Layin Dogo A Birnin Kano Na Naira Tiriliyan 1
Gwamnatin Tarayya ta amince da gina layin dogo na zirga-zirgar cikin birni a Kano, kan kuɗin da ya kai Naira tiriliyan ɗaya, domin inganta harkokin sufuri da rage cunkoson ababen hawa a babban birnin jihar.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mambobin tawagar jihar da suka halarci Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa ta shekarar 2025 da aka gudanar a Jihar Borno.
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Layin Dogo A Birnin Kano Na Naira Tiriliyan 1
A cewarsa, aikin layin dogon zai taimaka wajen bunƙasa harkokin tattalin arziki, sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kuma rage matsin lambar cunkoson ababen hawa a birnin Kano.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis ta ce amincewar da Gwamnatin Tarayya ta bayar na daga cikin manyan ayyukan raya ababen more rayuwa da ake shirin aiwatarwa a jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran aikin, idan aka kammala shi, zai samar da ayyukan yi tare da sauya fasalin sufuri a Kano.
