Connect with us

News

‎Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe N1.5trn Don Gyara Layin Dogo Mai Amfani Da Lantarki A Kano

Published

on

abuja light rail

‎Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kashe Naira tiriliyan 1.5 wajen gyara layin dogo jirgin ƙasa mai amfani da lantarki a Kano.

‎Shugaban Kwamitin Ƙasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar (Bichi), ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis.

Advertisement

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Yawaitar Hare-haren ’Yan Bindiga A Zamfara

‎Ya ce aikin, wanda darajarsa ta kai dala biliyan ɗaya, zai rage cunkoson ababen hawa, ya inganta zirga-zirgar mutane da kaya, tare da ƙara wa tattalin arzikin jihar ƙarfi.

‎ “Wadanda suka yi tafiya zuwa ƙasashen Turai da Asiya sun ga irin waɗannan ayyuka da tasirin su ga ci gaban birane. A nan Kano, wannan aikin zai haɓaka tattalin arziki matuƙa idan an kammala shi,” in ji Bichi.

Advertisement

‎Bichi ya ce maganar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya nuna kulawa ga Arewacin Najeriya ba ta da tushe. Ya ce shugaban ƙasar ya kaddamar da ayyuka da dama a yankin, ciki har da gyaran manyan tituna da harkokin sufuri, kiwon lafiya, noma da tsaro.

Advertisement

‎DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending