Connect with us

News

Gwamnoni 29 Sun Kashe Naira Biliyan 80 Kan Tafiye-Tafiye A Cikin Wata Shida

Published

on

Gwamnonin Najeriya

Wani sabon bincike ya gano cewa gwamnoni 29 na jihohi a Najeriya sun kashe akalla Naira biliyan 79.97 wajen yin tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen waje daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025.

Wannan adadi ya nuna karin kaso 14.72 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira biliyan 69.71 da aka kashe a irin wannan lokaci a shekarar 2024. Wannan lamari ya sake tayar da kura kan yadda ake ci gaba da yin almubazzaranci da kudaden jama’a a lokacin da yawancin jihohi ke cikin bashi, raguwar kudaden shiga, da dogaro da rabon gwamnati daga Asusun Tarayya.

Advertisement

‎Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe N1.5trn Don Gyara Layin Dogo Mai Amfani Da Lantarki A Kano

Binciken ya fito ne daga rahotannin aiwatar da kasafin kudi na zangon farko da na biyu na shekarar 2025 da aka samo daga shafukan yanar gizon jihohin.

Rahoton ya kuma gano cewa duk da irin wadannan kashe-kashen, jihohi kadan ne suka samu jarin kasashen waje a zangon farko na shekarar, abin da ya kara jefa tambaya kan amfanin irin wadannan tafiye-tafiyen wajen kawo ci gaba ga jihohi.

Advertisement

Kididdigar ta nuna cewa Lagos ce ta fi kashe kudi da N6.23bn, sai Osun (N6.21bn) da Kano (N5.58bn) wacce ta fi kashewa a Arewa. Taraba ta kashe N5.22bn, Bayelsa N3.78bn, Ekiti N3.76bn, Borno da Cross River duk N3.68bn, Yobe N3.70bn, yayin da Edo ta kashe N3.51bn.

Masana tattalin arziki da dama sun bayyana damuwa kan irin yadda ake ci gaba da kashe makudan kudade a kan tafiye-tafiye, suna gargadin cewa hakan na nuna gazawar tsare-tsaren raya kasa a matakin jiha, tare da bukatar a mayar da hankali kan aikin ci gaba mai amfani kai tsaye ga jama’a.

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending