Connect with us

News

Dole Gwamnonin Su fayyace wa ‘yan Nigeria yadda kuka kashe Naira Tiriliyan 40 kudaden kananan hukumomi – SERAP 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Kungiyar SERAP mai fafutukar Kare Hakkokin Tattalin Arziki da tabbatar da demokradiyya, ta yi zargin cewa gwamnonin jihohin Najeriya 36 da ministocin babban birnin tarayya Abuja, sun karkatar da Naira tiriliyan 40 da aka ware wa kananan hukumomi tun shakarar 1999.

SERAP ta bukaci gwamnonin da kuma ministan babban birnin tarayya Abuja na yanzu, Nyesom Wike, da su bayyana cikakken bayani kan kason da gwamnatin tarayya ke yi wa kananan hukumomi tun bayan komawar mulkin dimokradiyya.

Advertisement

Hukumar NDLEA na neman Tsohuwar Sarauniyar Kyau ta Nijeriya ruwa a jallo

SERAP ta kuma yi kira gare su “da su gaggauta gayyato Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawata EFCC da sauran Laifuka masu alaka da Hukumar Yaki ta’annati don binciki hakikanin yadda aka kashe kudaden da gwamnatin tarayya ta ware wa kananan hukumomin jihar ku da FCT tun daga watan Mayun 1999.”

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa mai dauke da kwanan wata 27 ga watan Janairu, 2024, mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan ta, Kolawole Oluwadare, SERAP ta bayar da hujjar cewa “’yan Najeriya na da ‘yancin sanin hakikanin yadda aka fitar da kudade da kuma yanda aka kashe kudaden da gwamnatin tarayya ke bayarwa” a kowace jiha da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Advertisement

A cewar SERAP, jihohi da babban birnin tarayya ya kamata a koyaushe su buga bayanan da suka shafi ainihin abin da suke kashewa kudin da gwamnatin tarayya ke warewa kananan hukumomi.

Kungiyar ta ce sakamakon binciken da ta gudanar ya nuna cewa jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja “sun tattara sama da N40tn na gwamnatin tarayya da aka ware wa kananan hukumomi 774 na kasar nan da kuma babban birnin tarayya Abuja”.

Advertisement

Oluwadare ya ce, “SERAP ta damu da cewa duk da dimbin arzikin man fetur da kasar ke da shi, talakawan Najeriya ba su amfana da kudin man fetur kadan saboda cin hanci da rashawa da ya karu, da kuma al’adar rashin hukunta masu laifi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending