Connect with us

News

Kungiyar likitocin Asibitin kwararru na Murtala Muhammad ta umarce mambobinta su dakatar aiki nan take 

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

Kungiyar likitocin Asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake jihar Kano ta bayar da Sanarwar cewar ta janye mambobinta daga bakin aiki har sai an sanar da su.

Rahotanni na nuni da cewa hakan ya faru ne Sakamakon yanda wasu ’yan daba dauke da muggan makamai suka kutsa kai cikin sashin masu kula da masu haihuwa na asibitin inda suka far wa wani likita da ke bakin aiki akan rasuwar yar uwar su a cikin Asibitn.

Advertisement

Dole Gwamnonin Su fayyace wa ‘yan Nigeria yadda kuka kashe Naira Tiriliyan 40 kudaden kananan hukumomi – SERAP 

Lamarin dai ya faru ne a yammacin ranar lahadi a asibitin kwararru na Murtala Muhammad

Hakan yasa kungiyar likitocin Asibitin suka dauke matakin dakatar da aikin su sabida rashin tsaro a cikin Asibitin.

Advertisement

Haka zalika sanarwar ta kara da cewa Shuwagabannin kungiyar sun tattaru zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka lura da rashin tsaro a duk asibitin. Hakan na kawo cikas ga tsaro da tsaron ma’aikatan lafiya a asibitin.

Kungiyar likitocin Asibitin sun ce za su cigaba da sanya ido kan yanayin tsaro ga mambobin kungiyar yadda ya kamata.

Advertisement

Dan hakan Dukkan membobin mu na kungiyar cewa Wannan sanarwar da aka umarce su da su daina aiki har sai an sanar dasu akan wannan yanayi mara kyau

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending