News
Wata Daliba Ta Hallaka Kanta Sakamakon Saurayin Ta Ya Nemi Su Rabu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata daliba mai suna Jamima Shetima Balami ta kashe kanta ta hanyar shan gubar ɓera a jihar Adamawa.
Jamima, wacce ta kasance ɗalibar National Diploma II a Sashen Sadarwa na Jama’a a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Mubi a Jihar Adamawa,kafin rasuwar ta tana samun horon masana’antu (IT) a gidan talabijin na Adamawa (ATV) da ke Yola.
Matashiyar ƴar kimanin shekaru 24, wacce ta kashe kanta ne lokacin da saurayin ta wanda yake malami ne a Jami’ar Modibbo Adama (MAU) ya bukaci su rabu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan jihar (PPRO), SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa da LEADERSHIP Faruwar lamarin a yau Litinin inda ya bayyana cewa mahaifin marigayiyar shi ne ya kai rahoton faruwar lamarin ga yan sanda.
