News
Gwamnoni Sun Goyi Bayan Kudurin Dokar Harajin Shugaba Tinubu
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta amince da Kudirin Gyaran Haraji, inda ta ba da shawarar cewa kada a kara harajin VAT kuma ta gabatar da muhimman shawarwari.
”Kungiyar ta amince da sabon tsarin raba kuɗin Harajin (VAT) domin tabbatar da daidaiton rarraba arzikin kasa kamar haka :
Kashi 50% bisa daidaito,
30% bisa la’akari da abin da aka samar,
20% bisa yawan jama’a.
”Mambobin sun amince cewa bai kamata a kara harajin VAT ba ko rage Harajin Kuɗin Shiga na Kamfanoni (CIT) a wannan lokaci, don kiyaye daidaiton tattalin arziki. Kungiyar ta nemi a ci gaba da ware kayan masarufi da kayan noma daga harajin VAT don kare walwalar ‘yan ƙasa da ƙarfafa aikin gona.
”Taron ya bayar da shawarar cewa bai kamata a saka sharadin kawo ƙarshen wa’adin TETFUND, NASENI, da NITDA a cikin rabon kudaden cigaba a kudirin dokar ba.
”Taron ya goyi bayan ci gaba da aikin majalisa a Majalisar Dokoki ta Kasa wanda zai kai ga kammala amincewa da Kudirin Gyaran Haraji”,
Acewar AbdulRahman AbdulRazaq, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya
