News
Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Yawaitar Hare-haren ’Yan Bindiga A Zamfara
Mazauna akalla kauyuka 30 daga Dan-Isa da Kagara, a karamar hukumar Kaura-Namoda, Jihar Zamfara, sun gudanar da zanga-zanga a Gusau, babban birnin jihar, a ranar Alhamis, domin nuna damuwarsu kan tsanantar hare-haren ’yan bindiga a yankinsu.
Masu zanga-zangar – ciki har da mata da yara – sun isa harabar gidan gwamnatin jihar dauke da alluna da ke ɗauke da rubuce-rubuce irin su: “Muna bukatar zaman lafiya a kauyukan Kaura-Namoda,” “Gwamna Dauda Lawal da Matawalle, ku kawo mana dauki,” da “Ana kashe mu kowace rana.”
NAHCON Ta Sanar Da Naira Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Ajiya Na Aikin Hajjin 2026
Jagoran masu zanga-zangar, Lawal Kamilu daga Dan-Isa, ya ce dalilin fitowarsu shi ne nuna fushi da rashin amincewa da yadda hare-haren ke ci gaba da kashe mutane da yin garkuwa da su.
“Mun fito daga kauyuka kusan 30 saboda mafi yawan mutanenmu ko dai an kashe su, ko kuma ’yan bindiga sun yi garkuwa da su. Suna bukatar kudin fansa mai tarin yawa, alhali ba mu da abin da za mu bayar. Mun sayar da dukkan kadarorinmu da gonakanmu wajen biyan kudin fansar ’ya’yanmu da ’yan uwanmu da aka sace a baya,” in ji shi.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin Bola Tinubu, da su gaggauta daukar mataki.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
