Connect with us

Politics

Akwai Yiwuwar Kwankwaso Ya Zama Abokin Takarar Tinubu A 2027

Published

on

FB IMG 1750722983638

Rahotanni da ga Jaridar  BUSINESS DAY na nuni da cewa Shugaba Bola Tinubu na iya sauya mataimakinsa Kashim Shettima da Sanata Rabi’u Kwankwaso a 2027.

Majiyoyi daga Abuja sun bayyana cewa hakan ne yasa Abdullahi Ganduje bai marawa Shettima baya ba a taron jam’iyya da aka yi a Gombe.

Advertisement

Iran ta yi wa sansanonin sojojin Amurka da ke Qatar da Iraqi luguden makamai masu linzami

Wata majiya daga APC ta ce Kwankwaso yana samun goyon bayan jiga-jigan jam’iyyar domin ƙarfafa damar zarcewar Tinubu a zaɓen 2027.

Majiyar ta ce an fara tattaunawa da Kwankwaso, kuma ya kai ziyara ga Shugaban ƙasar domin samun goyon bayansa cikin ƙanƙanin lokaci.

Advertisement

Kwankwaso na da tasiri sosai a Arewa ta hanyar ƙungiyar Kwankwasiyya, lamarin da ke jan hankalin shugaban ƙasa Tinubu da jam’iyyar APC.

Tsohon Gwamnan Kano wanda yayi mulki sau biyu, Kwankwaso, shi ne jagoran jam’iyyar NNPP wacce ke mulkin jihar Kano a halin yanzu.

Advertisement

Ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Tsaro a zamanin Obasanjo, kuma ya wakilci Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.

Masu tsara siyasar Tinubu na duba yadda za su lashe zabe a Kano dake da ƙananan hukumomi 44 da masu kaɗa ƙuri’a sama da miliyan biyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending