Politics
Atiku Da Wasu Jiga-jigan Siyasa Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi Inec Ta Yi Musu Rajista
Wasu fitattun ‘yan siyasa a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, sun kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna All Democratic Alliance (ADA), tare da aike da buƙatar rajista zuwa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
Rahotanni sun bayyana cewa an aike da takardar neman rajistar jam’iyyar ne a ranar 19 ga Yuni 2025, yayin da aka karɓe ta a ofishin INEC washegari. Wannan na nuna cewa sabuwar ƙungiyar siyasar ta fi son kafa sabuwar jam’iyya kai tsaye maimakon haɗewa da wata jam’iyya da ke wanzuwa.
Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, da Dr Umar Arɗo — wanda shi ne kodinetan ƙungiyar League of Northern Democrats kuma tsohon mataimaki ga tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo — na daga cikin jiga-jigan da suka mara wa wannan ƙungiya baya.
Gwamnatin Kano Za Ta Fara Tantance Malaman BESDA Don Daukar Aiki Na Dindindin
Ƙungiyar ta bayyana cewa kafa ADA na da nufin samar da sabuwar dama ga ‘yan Najeriya da ke nuna rashin gamsuwa da halin da ƙasar ke ciki a yanzu, da kuma ƙoƙarin dakile sake tsayawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Sai dai a makonnin baya-bayan nan, INEC ta sake tunatar da ƙungiyoyin siyasa game da buƙatar bin doka da ƙa’ida wajen kafa jam’iyyu ko gudanar da shirye-shiryen zaɓe, tana mai cewa babu damar yin wasa da tsarin doka.
Takardar buƙatar rajistar jam’iyyar ADA ta samu sa hannun shugaban wucin-gadin jam’iyyar, Cif Akin A. Rickets, da sakataren wucin-gadi, Abdullahi Elayo.
