News
Gwamnatin Kano Za Ta Fara Tantance Malaman BESDA Don Daukar Aiki Na Dindindin
Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB) ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen fara tantance malaman da ke aiki ƙarƙashin shirin BESDA, da nufin ɗaukar su aiki na dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na hukumar, Balarabe Danlami Jazuli, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Malam Yusuf Kabir, a ranar Alhamis, 19 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa za a gudanar da jarrabawar tantancewar a matakin shiyyoyi, inda aka bukaci dukkan malaman BESDA da ke cikin jerin sunayen da aka fitar, su tuntubi sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomin da suke aiki domin samun cikakken bayani game da wuraren da za a gudanar da jarrabawar.
SUBEB ta kuma bayyana cewa dole ne mahalarta su je da takardun da suka haɗa da: asalin takardar ɗaukar aiki ta BESDA, katin corhot 4, lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN), da kuma biro domin amsa tambayoyi.
Hukumar ta gargadi cewa duk wanda ba ya cikin tsarin kada ya kuskura ya halarci jarrabawar, tare da yi wa malaman fatan nasara a gwajin dake tafe.
