News
Koriya Ta Arewa Ta Goyi Bayan Iran, Ta Soki Isra’ila
Koriya ta Arewa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Iran, tana mai caccakar Isra’ila bisa hare-haren da take kai wa a yankin Gabas ta Tsakiya.
A wata sanarwa da kafar gwamnati ta Koriya ta Arewa, KCNA, ta fitar, ƙasar ta ce tana “damuwa ƙwarai” da yadda Isra’ila ke kai hare-hare kan fararen hula, cibiyoyin nukiliya da kuma tashoshin makamashi a Iran.
Majalisar Dattawa Ta Bukaci NNPCL Ya Bayyana Inda Naira Tiriliyan 210 Ta Shige Cikin Mako Guda
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ya bayyana matakin da Isra’ila ke ɗauka a matsayin “laifi ga bil’adama” kuma “abin da ba za a iya yafewa ba”.
Ya ce Isra’ila na aikata “ta’addancin da wata ƙasa ke ɗaukar nauyinsa”, yana mai cewa hakan na ƙara haifar da barazanar “barkewar sabon yaƙi a dukkan sassan yankin”.
Koriya ta Arewa na jan kunnen Amurka da ƙawayenta
Sanarwar ta kuma zargi Amurka da ƙawayenta na Yamma da ruruta wutar rikicin, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya haifar da mummunan rikici da ba za a iya shawo kansa ba.
“Isra’ila tana karɓar goyon baya daga Amurka da ƙasashen Yamma, kuma hakan na nuna cewa ƙasar ta zama wata barazana ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya,” in ji sanarwar.
Koriya ta Arewa ta ce ƙasashen duniya na kallon yadda Amurka da abokan tafiyarta ke ƙin amincewa da Iran ta kare kanta, duk da hare-haren da ake kai mata.
Trump ya ce haƙurinsa ya ƙure
Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa haƙurinsa ya kai ƙarshe game da lamurran da suka shafi Iran.
Koriya ta Arewa ta ce matakin da Amurka da ƙawayenta suka ɗauka na iya tura rikicin yankin zuwa wani “mataki na bala’i” wanda duniya ba za ta iya shawo kansa ba.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
