News
Majalisar Dattawa Ta Bukaci NNPCL Ya Bayyana Inda Naira Tiriliyan 210 Ta Shige Cikin Mako Guda
Majalisar Dattawa ta bukaci Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, wato NNPCL, da ya bayyana cikin gaggawa inda aka karkatar da kuɗaɗe kimanin Naira Tiriliyan 210 da aka gano cikin rahotannin kasafin kamfanin daga shekarar 2017 zuwa 2023.
Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kuɗaɗen al’umma ne ya gano wannan gagarumin gibin, inda ya nuna shakku a kan yadda wasu kudade suka shigo da kuma yadda wasu aka kashe ba tare da cikakken bayani ba.
Rundunar Yaƙi Da Fadan Daba A Kano Ta Zargi ‘Yan Siyasa Da Tallafa Wa Ƴan Daba
Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ya bayyana cewa bayanan da NNPCL ta gabatar sun nuna cewa akwai abubuwan da suka sabawa juna, sannan kuma ba su da ma’ana, tare da alamun rashin gaskiya da boye gaskiya.
Wannan ci gaba na zuwa ne a lokacin da ake kara tursasa bukatar ladabtar da manyan kamfanonin gwamnati da ke cin kuɗin al’umma babu wani ingantaccen bayani.
An dai gayyaci wasu manyan jami’an NNPCL, ciki har da Dapo Segun, shugaban sashen kula da kuɗaɗe na kamfanin, inda suka bayyana a gaban kwamitin Majalisar a zaman ranar Laraba.
A cewar kwamitin, bayan haɗa adadin kuɗaɗen da aka ce an kashe a wasu ayyuka da kuma kwangiloli ba tare da cikakken bayani ba, kuɗin sun kai Tiriliyan Naira 210.
Sanata Wadada ya ce, “Wannan lamari ba zai wuce haka ba. Kwamitin ya mika tambayoyi 11 zuwa ga NNPCL, kuma muna jiran su gabatar da amsoshi cikin mako guda kacal.”
Majalisar ta bayyana cewa zata dauki matakin da ya dace idan NNPCL ta gaza bayar da cikakken bayani mai gamsarwa, duba da irin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki da kuma yawan bashin da ake fama da shi.
Wannan tambaya na iya jefa tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, cikin sabon bincike, kasancewar ya shugabanci kamfanin daga shekarar 2019 zuwa 2025, lokacin da mafi yawan waɗannan kuɗaɗe suka shige.
