News
Rundunar Yaƙi Da Fadan Daba A Kano Ta Zargi ‘Yan Siyasa Da Tallafa Wa Ƴan Daba
Rundunar tsaro ta musamman da ke yaƙi da fadan Daba da fashi da makamin da kuma Kwacen waya a jihar Kano, ta bayyana cewa wasu ‘yan siyasa na daga cikin masu ɗaukar nauyin ƴan Daba, lamarin da ke ƙara ta’azzara matsalar a fadin jihar.
Kwamandan rundunar, Inuwa Salisu Sharada, ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da hannu wajen ɗaukar nauyin waɗannan matasa da ke haddasa rikice-rikice a unguwanni daban-daban.
Jami’ar ABU Ta Haramta Sanya Matsattsun Kaya Da Runguma A Farfajiyar Makaranta
“A halin yanzu muna bibiya tare da gudanar da bincike kan matasan da suka addabi jama’a da fadan Daba da fashi da Kwacen waya a Kano. Manufarmu ita ce gano ‘yan siyasar da ke tallafa wa ayyukansu, domin ɗaukar matakin da ya dace,” in ji kwamandan.
Ya ce abin takaici ne yadda galibin matasan da ke aikata irin wannan laifi yara ne ‘yan kasa da shekaru 15, inda ya yi kira ga iyaye da su ƙara sanya ido tare da tsawatar wa ‘ya’yansu.
“Ina jan hankalin iyaye da su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu, domin duk wanda aka kama da laifi, za a ɗauki matakin doka a kansa ba tare da la’akari da shekarunsa ba,” in ji Sharada.
A wani bangare na ƙoƙarin kawo karshen wannan matsala, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya kaddamar da sabbin dabaru na yaƙi da fadan Daba, Kwacen waya da shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan wata ganawa da ya yi da manyan jami’an rundunar a ranar Asabar da ta gabata, inda suka tattauna hanyoyin da za su bi wajen dakile wannan barazana ga zaman lafiya a jihar Kano.
