News
Kotu Ta Aika Wa Shugaban INEC Takardar Tuhuma
Kotun tarayya da ke Abuja ta aika wa shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, takardar tuhuma kan raina umarnin kotu.
Jam’iyyar NRM ce ta shigar da ƙarar, inda ta zargi shugaban INEC da ƙin aiwatar da umarnin da kotu ta bayar.
Gwamnatin Kano Za Ta Fara Tantance Malaman BESDA Don Daukar Aiki Na Dindindin
Ayuba Sule ne ya miƙa takardar zuwa ofishin INEC da ke Abuja a ranar Alhamis, bisa umarnin da Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya bayar tun ranar 17 ga Yuni.
Takardar da aka fi sani da Form 48, na bayyana mataki na farko da ake ɗauka kan wanda ya ƙi bin hukuncin kotu.
A cewar wani bayani da kakakin jam’iyyar NRM na ƙasa, Anselem Nebeife, ya fitar, jami’an INEC sun ƙi karɓar takardun daga mai kai sammaci.
Daga bisani sai ya ajiye takardun a gaban ofishin sashen shari’a na hukumar.
Kotun ta bayar da umarnin a miƙa takardun ta hanyar da ba kai tsaye ba, bayan buƙatar da lauyan jam’iyyar NRM, Oladimeji Ekengba, ya shigar.
Lauyan ya ce hukumar INEC ta yi biris da hukuncin da kotu ta bayar tun ranar 5 ga Maris.
Hukuncin ya umarci INEC da ta amince da sakamakon babban taron gaggawa da jam’iyyar ta gudanar a ranar 17 ga Janairu, wanda aka zaɓi Chief Edozie Njoku a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.
A cewar jam’iyyar, taron ya gudana ne domin gyara matsaloli da cike guraben shugabanci a cikin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta zargi INEC da yin watsi da umarnin kotu da gangan, duk da cewa tana da cikakken sani game da abin da umarnin ya ƙunsa.
Kotun ta saka ranar 15 ga watan Yuli domin ci gaba da sauraren shari’ar.
