News
Iran Ta Lalata Cibiyar Kimiyya Mafi Muhimmanci A Isra’ila
Iran ta kai hari da makami mai linzami kan cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke kusa da birnin Tel Aviv, a Isra’ila — wadda ake ɗaukarta a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin binciken kimiyya mafi muhimmanci a ƙasar.
Rahotanni sun ce harin ya auku ne da safiyar Asabar, inda wani gini da ke ɗauke da dakunan gwaje-gwaje na zamani ya rushe gaba ɗaya, yayinda gobara ta tashi a wasu sassan cibiyar. Babu wanda ya mutu ko ya ji rauni a harin, domin ba kowa a cikin ginin a lokacin da makamin ya faɗo.
Cibiyar ta Weizmann ta tabbatar da cewa an yi asarar dukiya da aka kiyasta da kimanin dala miliyan 500 sakamakon harin, lamarin da ya tilasta masu bincike gudu domin ceto kayayyakin aiki daga cikin ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe.
Harin dai na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya bayan hare-haren da Isra’ila ta kai kan Iran, harin da ya kashe masana kimiyyar nukiliya da wasu manyan jami’an tsaron Iran.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya kai ziyara wurin da harin ya auku, inda ya ce:
“Harin ya nuna dalilin da ya sa ba za mu taɓa bari Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.”
A baya-bayan nan ne Isra’ila ta kai hari kan Iran, tana zargin cewa Tehran na dab da ƙera makaman nukiliya. Iran ta musanta zargin, tana mai cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne kawai.
Sai dai a matsayin martani, Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuƙa kan wasu wurare a Isra’ila, inda ta ce ba za ta zuba ido ana ci gaba da kai mata hari ba.
Duk da cewa cibiyar binciken Weizmann na gudanar da bincike a fannoni irin su kimiyya da kiwon lafiya, tana da alaƙa da tsaro, musamman tun bayan da ta sanar da haɗin gwiwa da kamfanin tsaron Isra’ila, Elbit Systems, a watan Oktoban 2024 domin nazarin “kayayyakin da aka samo daga halittu don amfani da su a harkokin tsaro”.
A halin yanzu, Iran ta bayyana cewa ba za ta koma teburin tattaunawa kan shirin nukiliyarta ba, duba da yadda take fuskantar hare-hare daga Isra’ila. Yunkurin ƙasashen Turai na ganin Tehran ta amince da sabuwar tattaunawa bai haifar da wani sakamako ba a halin yanzu.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
