News
Wata Motar Jigilar Fasinja Mai Amfani Da CNG Ta fashe A Kaduna
Wata motar jigilar fasinja mai amfani da iskar gas ta CNG ta fashe a safiyar Lahadi a tashar motoci ta Mando da ke birnin Kaduna, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Motar, wadda aka fi sani da “Luxurious Bus”, mallakin wani kamfanin sufuri mai suna Silver, dake gudanar da zirga-zirga tsakanin Kudancin da Arewacin Najeriya.
Radio Kano ta ruwaito cewa fashewar ta faru ne da misalin asubahin ranar, a lokacin da babu fasinjoji ko ma’aikata a cikin motar.
Ko da yake babu asarar rai ko samun raunuka, fashewar ta haddasa asarar dukiya, inda wasu ƙananan motoci da ke kusa da wurin suka lalace sakamakon ƙarfin fashewar.
Har yanzu ba a bayyana musabbabin fashewar ba, yayin da ake sa ran hukumomi za su fara bincike domin gano dalilin faruwar lamarin.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙara amfani da motocin da ke amfani da iskar gas ta CNG a Najeriya, matakin da ke janyo muhawara kan batutuwan tsaro da kulawa da irin waɗannan motoci.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
