News
Jigawa: ‘Yansanda Sun Kama Matashi Kan Zargin Kona Mahaifinsa Har Lahira A Kazaure
Rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa ta kama wani matashi mai suna Kabiru Nuhu mai shekaru 27 bisa zargin hallaka mahaifinsa mai shekaru 60 ta hanyar kona shi da wuta a karamar hukumar Kazaure.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Afrilu a unguwar Lokon Malamai da ke kusa da rukunin gidaje na Magama a cikin garin Kazaure.
Dakarun Soji Sun Ceto Mutum 31 Da Aka Sace Daga Cocin Kaduna
Ya ce rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin da misalin karfe 6:30 na safe, inda nan take aka tura jami’ai zuwa wurin domin daukar matakin gaggawa. Jami’an sun garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibiti domin ceto rayuwarsa, sai dai likitoci sun tabbatar da rasuwarsa.
A cewar kakakin rundunar, binciken farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne kimanin mintuna 30 kafin a kai rahoto, inda ake zargin matashin ya zuba wani abu mai saurin kamawa da wuta — wanda ake kyautata zaton man fetur ne — a jikin mahaifinsa kafin ya cinna masa wuta.
Bincike ya kai ga cafke wanda ake zargin, inda aka same shi da raunuka a goshinsa, hannaye da kuma yatsun kafa, lamarin da ke kara karfafa zargin hannu a cikin wannan aika-aika.
Rundunar ta ce a halin yanzu wanda ake zargin yana tsare, kuma za a mika shi zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse domin zurfafa bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Haruna Alaba Yahaya, ya yi Allah-wadai da wannan lamari, yana mai jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci irin wannan aika-aika ba.
Haka kuma, ya bai wa al’ummar jihar tabbacin cewa za a tabbatar an yi adalci a kan lamarin.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
