News
Dakarun Soji Sun Ceto Mutum 31 Da Aka Sace Daga Cocin Kaduna
Sojojin Najeriya sun ceto masu ibada 31 da ‘yan ta’adda suka sace daga wani coci a ƙauyen Ariko da ke ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna, bayan gaggawar kai dauki sakamakon kiran neman taimako.
PREMIUM TIMES ta ruwaito a baya cewa ‘yan ta’adda sun kai hari kan wasu coci biyu, inda suka kashe akalla mutum bakwai tare da sace wasu da dama.
KANO: Jinkirin Diyya Ya Jefa Manoma A Albasu Cikin Mawuyacin Hali
Harin ya faru ne a lokacin ibadar Ista a Cocin ECWA na Farko da kuma Cocin Katolika na St. Augustine. Sai dai rundunar sojin ta tabbatar da harin ne kawai a kan cocin ECWA.
A cewar sojojin, dakarunsu sun dauki mataki ne bisa sahihan bayanan sirri tare da hadin gwiwar mazauna yankin, inda suka bi sawun maharan zuwa dazukan da ke kewaye.
Sanarwar ta ce dakarun sun fafata da ‘yan ta’addan da suka rika tserewa a wata mummunar arangama, inda suka rinjaye su da karfin wuta.
Wuta mai tsanani da sojojin suka yi ya tilasta wa maharan barin mutane 31 da suka sace, ciki har da mutum guda da ya jikkata, wanda a yanzu yake karbar magani.
Rundunar sojin ta ce mutane biyar sun rasa rayukansu a harin, kuma an gano gawawwakin su a wurin da lamarin ya faru. Haka kuma, jinin da aka gani a hanyoyin da maharan suka bi yayin tserewa na nuna cewa sun samu munanan raunuka a yayin artabun, in ji sanarwar.
Sojojin sun sake jaddada kudurinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da tsaron kasa, inda suka bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin tallafa wa ayyukan tsaro da ke gudana.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
