Opinion
Bankwana Ga Marigayi Hazikin ‘Dan Jarida, Kwamared Aliyu Abubakar Getso: Rayuwa Ta Hiddima, Tawali’u Da Sadaukarwa
Inna lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un
Alƙalami ya bushe, makirufo ya yi shiru, amma murya da jarumta da gagarumar gudunmawar marigayi Kwamrade Aliyu Abubakar Getso za su ci gaba da wanzuwa a cikin zukatan duk wanda ya san shi.
Da safiyar Lahadi, 5 ga Oktoba, 2025, labarin rasuwar ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jaridu, gogaggen mai watsa shirye-shirye a gidan radiyo kuma jigo a harkar ƙwadago ya bazu cikin Kano da kewaye.
Gidajen radiyo, da kafafen sada zumunta da shafukan yanar gizo suka cika da labarai da ta’aziyya ga “Baba Getso”, wanda ya kasance sunan da matasan ‘yan jarida kan kira shi.
Tsarin Bashin Kuɗin Karatu A Jami’o’i Ya Haifar Da Tsadar Kuɗin Rijistar Ɗalibai —Rahoto
Asalin Rayuwa Aliyu Abubakar Getso:
An haifi Aliyu Abubakar Getso a shekara ta 1956 a garin Getso, ƙaramar hukumar Gwarzo, Jihar Kano.
Yana daga cikin zuriyar sarauta ta San-Getso, kuma ɗan marigayi Malam Abubakar, Chiroman Getso (Sidi), wanda shi ne Dagaci garin Getso a lokacin.
Rayuwarsa ta kasance mai tawali’u, cike da natsuwa, da kuma kishin al’umma da son gaskiya.
Tarihin Ilimi da Aikin Sa:
Marigayi Aliyu Getso ya fara karatun Alƙur’ani a garin Getso, kafin ya shiga makarantar Firamare ta (Gwarzo Boarding Primary School) daga 1962 zuwa 1968. Daga nan ya wuce Makarantar gaba da Firamare ta Dambatta, (Government Secondary School Dambatta) daga 1969 zuwa 1974.
Bayan haka ya halarci Makarantar Share fagen shiga Jami’a ta Gwamnatin Tarayya dake Mubi, jihar Adamawa (Federal School of Arts and Science), Mubi, daga 1975 zuwa 1977, sannan ya samu halartar makarantar kammala horon Watsa Shirye-shiryen na Talabijin (TV Broadcast Course) a Landan, Ingila a shekara ta 1981.
Ya fara aikin gwamnati a Ma’aikatar yaɗa labarai ta Jihar Kano a shekara ta 1977, inda ya yi aiki da cikakken sadaukarwa har zuwa lokacin da ya yi ritaya a 1999.
Bayan ritayarsa, ya ci gaba da hidimar aikinsa da kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu kamar Freedom Radio, Vision FM, da Premier Radio Kano, inda ya bar tarihin da ba za a manta da shi ba.
“ Ni ina daga cikin waɗanda na samu horon aikin jarida daga hannun Baba Getso ya koyar da mu yadda ake yin aikin jarida da gaskiya, da cikakken mutunci.”
Gudunmawarsa Ga Kungiya ‘Yan Jarida da kuma Kungiyar Kwadago A Kano:
Baya ga aikin jarida, Comrade Getso ya kasance jigo a ƙungiyoyin ma’aikata a inda ya rike mukamai kamar haka:
Sakataren Kungiyar ‘yan jaridu reshan Ma’aikatar Yaɗa labarai ta Kano, (NUJ Information Chapel) daga 1986 zuwa 1988,
Sakataren na ƙungiyar ‘yan jaridu na jihar Kano baki ɗaya,(NUJ Kano State Council), daga 1992 zuwa 1996,
Ya kuma zama mataimakin Sakataren Kungiyar Kwadago reshan jihar Kano (NLC Kano State Chapter).
A waɗannan mukamai, ya nuna gaskiya da jarumtaka, da jajircewa wajen kare muradun ma’aikata, ba tare da tsoron faɗar gaskiya ba.
Aiki da Gaskiya da Girmamawa:
A matsayinsa na Shugaban Sashen Watsa Shirye-shirye, a Ma’aikatar Yaɗa labarai ya kasance mai shirya shirin “Jihar Kano A Yau”, ɗaya daga cikin shirye-shiryen rediyo mafi tsayi a tarihin Kano.
A ƙarƙashinsa ne na fara koyon aikin jarida a shekarar 1990, tare da jagorancin Malle Balarabe, inda suka riƙa ba mu horo ni da takwarorina kamar Mustapha Namadi Ringim, Idris Zakariyau Zaura, da wasu da dama.
Zan iya tuna manyanmu a wannan sashi kamar Malam Surajo Ibrahim Gaya da Marigayi Alhaji Auwalu Zubairu Chedi da Abdullahi Abubakar Tudunwada, da Marigayi Sule Maiganji Danbatta, wato dereban da ke jigila da mu domin samo labarai tun a tsohuwar jihar Kano.
Waɗannan shekarun sun zama makarantar rayuwa a gare mu — makarantar da Baba Getso ke koyar da halin kirki, da aiki tukuru, da juriya gami mutuntaka.
Rasuwa da Jana’izasa:
An gudanar da Sallar Jana’izarsa da misalin ƙarfe 9:30 na safe, a gidansa dake kusa da Kabuga ‘Second Gate’, Janbulo, a Kano, ƙarƙashin jagorancin Limamin Unguwar Janbulo.
Dubban jama’a suka halarci jana’izar, waɗanda suka haɗar da iyalai da abokai da abokan aiki, da manyan mutane da ‘yan jaridu daga Kano da ma sauran jihohi, domin raka shi zuwa makwancinsa na ƙarshe, sn bune shi a maƙabartar Dandali dake Goron dutse.
kwamrade Getso, ya mutu cikin mutunci, ya bar tarihi mai daraja. Kuma ayyukansa za su ci gaba da zama abin tunawa.
Halayensa da Ƙimarsa:
Marigayi Kwamarde Aliyu Getso mutum ne mai addini da nutsuwa da zuminci da tawali’u, da kuma gaskiya.
Ya kasance mai kishin aikinsa, mai tsaiwa a kan abin da yake na gaskiya kuma komai wahala.
Ya fi son gaskiya fiye da yabo, kuma ya rayu da tawali’u da nutsuwa gami da kamun kai.
Ga matasa, shi malami ne, aboki, kuma uba. Har zuwa mutuwarsa yana da shekaru 69, ya kasance mai kula da iyalansa, ya bar mata uku da ‘ya’ya da jikoki masu yawa, waɗanda za su ci gaba da ɗaukar darasin da ya bari na gaskiya da aiki tukuru da gaskiya.
Ƙarshe: Kira Ga Manazarta
Rasuwarsa babban rashi ne ga al’ummar jahar Kano da kafofin yaɗa labarai da ƙungiyar ‘yan jaridu da ƙungiyar ƙwadago, ba kawai a Kano ba, har ma a faɗin ƙasa baki ɗaya.
Alhaji Aliyu Getso ya tafi amma murya da ɗabi’unsa za su ci gaba da amsawa cikin zukatan mu.
Allah Ya gafarta masa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya ba shi Aljannatul Firdaus.
Ya kuma ba iyalansa da abokansa haƙurin jure wannan rashi mai girma.
Yau kwana uku ba ma tare da kai, Comrade — ka amsa kiran Mahalicci, ka tafi tafiyar da babu dawowa.
Sai mun haɗu a Darussalam, Baba Getso — muryar talakawa, jarumin ‘yan jarida, kuma jagoran da zuciyarsa ke cike da alheri.
Kofar Na’isa, tsohon Ma’aikacin Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Kano, yanzu kuma Adita/Mawallafi na jaridar The Stentor News Online.
