Connect with us

News

Gwamnatin Nijar Ta Dakatar Da Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu Kusan 3,000

Published

on

IMG 20260423 001017 928

Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta dakatar da ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu guda 2,900, daga cikin jimillar ƙungiyoyi 4,700 na gida da na waje da ke da rajista a ƙasar, kamar yadda ministan cikin gidan ƙasar, Mohamed Toumba ya bayyana.

Tun daga watan Yulin shekarar 2023, gwamnatin soji, ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani ta mayar da batun ikon mulkin ƙasa a matsayin babban al’amari da ta sa gaba, kamar yadda maƙwabciyarta kuma aminiyarta ƙasar Burkina Faso, wadda ita ma sojoji ne ke mulkarta ta yi.

Advertisement

Fashewar Tankar Mai Ta Hallaka Mutane 12, Ta Jikkata 38

A makon da ya gabata, mahukuntan Burkina Faso sun rushe tare da haramta ayyukan ƙungiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu fiye da 100, waɗanda akasarin su ke fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam.

Advertisement

A Jamhuriyar Nijar, akai-akai sojoji suke zargin ƙungiyoyi masu zaman kansu da rashin gaskiya wajen gudanar da ayyukansu da kuma tallafa wa rukunonin masu ɗauke da makami da ke tada ƙayar baya a sassan ƙasar daban-daban.

A shekarar da ta gabata, mahukuntan sun dakatar da wasu ƙungiyoyi na gida da na ƙasashen waje, su na mai nuni da rashin wallafa bayanan kuɗaɗen su na shekarar 2024 akan lokaci a mujallar sanarwar gwamnati.

Advertisement

Yayin da yake jawabi ta gidan talabijin na ƙasar a yammacin ranar Talata, Janar Mohamed Toumba ya bayyana cewa adadin ƙungiyoyin ya ragu daga 4,700 zuwa 1,800.

Akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa fiye da 330 da ke da rajista a Nijar, sai dai ba a tantance adadin waɗanda matakin ya shafa ba.

Advertisement

Toumba ya ƙara da cewa wannan matakin wani bangare ne na shirin tantancewa da kuma karkata akalar ƙungiyoyin zuwa ga ayyukan da suka dace da manufofin ci gaban ƙasa.

A cewar alƙaluman hukuma, ƙungiyoyin masu zaman kansu sun tara fiye da biliyan 250 na kuɗin CFA kwatankwacin dala miliyan 448 a shekarar 2024.

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending