News
An gurfanar da wani matashi a kotu bisa zargin kashe abokinsa saboda Bluetooth a Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An gurfanar da wani matashi a kotu a Kano bisa zargin kashe abokinsa saboda naurar sauraren sauti ta Bluetooth.
Ana zargin matashin ya caka wa abokin nasa mai suna Abdulazeez Aliyu, wuka a ciki ne, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Rundunar Ƴan sanda sun kama tsohon kansilan da wasu Mutum hudu bisa zargin yin fashi
Takardar karar ta bayyana cewa tun da farko wata sa-in-sa ce ta shiga tsakanin abokan biyu a kan abin saurare na wayar hannu (Bluetooth).
Aminiya ta ruwaito cewa wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumar sa da aikatawa na kisa wanda, ya saba da sashe na 221 a Kundin sharia na Pinal Kod.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Ibrahim Galadanchi, ta Kotun Majistare Mai Lamba 19 da ke zamanta a Nomanslan ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan yari.
Daga nan ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Janairu, 2023.
A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Cafke Mata Da Mijinta Tareda Makwabcinsu Bisa Zargin Su Da Aikata Laifin Kisan Kai A Kano
Majalisar dokokin Faransa ta zartar da dokar hana ɗaliban Najeriya da da na sauran ƙasashe shigowa da iyalansu ƙasar.
Bayan da aka amince da wani sabon lafazin ƙudurin, wannan matakin ya sami goyon baya daga jam’iyyar Renaissance ta shugaba Emmanuel Macron da kuma jam’iyar National Rally ta Marine Le Pen.
Manufofin shige da ficen da aka yi wa kwaskwarima na tsaurara matakai kan haɗuwar dangi, ta hana ‘yan ci-rani damar samun waɗansu ababen more rayuwa, da kuma haramta tsare yara ƙanana a wuraren tsare mutane.
Sai dai kuma shugabanni daga kashi ɗaya bisa uku na yankunan Faransa sun bayyana ƙin aiwatar da wasu muhimman matakai na doka.
Musamman ma, wani ɓangaren dokar yana banbance tsakanin ‘yan ƙasa da baƙi, gami da waɗanda ke zaune bisa doka a Faransa, dangane da cancantar samun waɗansu fa’idoji..
