Connect with us

News

Babban Hafsan Sojojin Libiya Ya Rasu A Hadarin Jirgin Sama A Turkiyya

Published

on

418189

Firaministan Libiya, Abdulhamid Dbeibeh, ya tabbatar da rasuwar Babban Hafsan Sojojin ƙasar, Muhammad Ali Ahmad al-Haddad, tare da wasu mutane hudu a wani haɗarin jirgin sama da ya faru kusa da babban birnin Turkiyya, Ankara.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin saman ya yi hatsari ne yayin da yake kan hanyarsa daga Istanbul zuwa Ankara, inda ya kama da wuta bayan yin saukar gaggawa. Hukumomin Turkiyya sun tura jami’an ceto zuwa wurin don gudanar da bincike da kuma taimakawa wajen gano dalilin haɗarin.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Kama Wasu ’Yansanda Bisa Kin Bin Umarnin Shugaba Tinubu Na Janyewa Daga Gadin VIP 

Firaminista Dbeibeh ya bayyana cewa mutuwar Janar al-Haddad babban rashi ne ga rundunar sojin Libiya da ƙasar baki ɗaya, yana mai bayyana shi a matsayin jarumi mai kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Libiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending