Connect with us

News

Kotu Ta Tsare Likita Mai Shekaru 72 Bisa Zargin Satar Yaro Da Siyar Da Shi 

Published

on

Kotu
Spread the love

Wata Kotu da ke sauraron ƙararrakin yara da laifukan mata a Awka, dake jihar Anambra, ta bada umarnin tsare wani likita mai shekaru 72 da wasu mata biyu bisa zargin satar yaro da siyar da shi ba bisa ƙa’ida ba.

Wadanda ake tuhuma sun haɗa da Dr. Daniel Ikebuilo, mai shekaru 72 da haihuwa; Ifunanya Ogbonna, mai shekaru 23; da Chidiogo Ogbonna, mai shekaru 20.

Asibitin Best Choice Zai Fara Manya Manyan Tiyatu Akan Kuɗi Kaso 50% Bayan Fara Bude Fayil Kyauta Da Rage Kuɗin Ganin Likita Da Ayyukansu

An gurfanar da su a gaban Alƙali U.E. Onochie bisa zargin haɗin baki wajen satar yaro da kuma ciniki da rayuwar yaro, abin da ya sabawa dokokin jihar Anambra.

Sai dai dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta laifin da ake zargin su da shi a gaban kotu.

Advertisement

Alƙalin kotun ya bada umarnin a tsare su a gidan gyaran hali na Awka, tare da dage cigaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga watan Agusta domin yanke hukunci kan buƙatar beli.

A cewar lauyar gwamnati, Sifeta Chinyere Okechukwu, ta shaida wa kotu cewa lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Afrilu, a unguwar Okpoko da ke Onitsha, inda matan biyu suka yaudari mahaifiyar yaron, Kosarachukwu Okpala, suka sace shi.

Rahoton ya nuna cewa Dr. Ikebuilo ya sayi yaron daga hannun matan biyu kan Naira 700,000, sannan daga bisani ya sake sayar da yaron a kan Naira miliyan 2 da dubu 300.

Ana tuhumar su da laifin da ya saba da sashe na 495 da 274 na dokar laifuka ta jihar Anambra ta 1991, da kuma sassa na dokar kare haƙƙin yara ta 2004 da dokar hana cin zarafin mutane ta 2017.

Advertisement

 

 

WIKKI TIMES

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *