Connect with us

News

Shugaban Amurka Tare Da Mataimakinsa Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Harin Bindiga

Published

on

Donald trump

Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, tare da Mataimakinsa, JD Vance, sun tsallake rijiya da baya a wani harin bindiga da aka kai a wurin taron da yake halarta.

Jami’an tsaro sun tsere da Mista Trump da JD Vance, bayan da wani ɗan bindiga ya buɗe wuta a lokacin da ake tsaka da taron likafar ’yan jarida masu aiki a Fadar Whitda Otel din Washington Hilton a ranar Asabar da dare.

Advertisement

DIYYAR NAIRA BILIYAN ƊAYA: Ko Kwandala Ba Zan Ba Yahaya Bello —Natasha Akpoti-Uduaghan

Mahalarta taron sun yi ta ɓoyewa a ƙarƙashin tebura domin tsira da ransu, a yayin da ɗan bindigar ke ɓarin wuta da muggan makamai a wurin taron da Fadar White House ta shirya.

Advertisement

Hukumar Leƙen Asiri ta Amurka ta ce maharin ya harbi wani jami’inta da ke kusa da shi, amma jami’in bai mutu ba, rigar sulken jikinsa ta kare shi.

Ta ƙara da cewa daga bisani jami’an hukumar sun yi nasarar kama ɗan bindigar, kuma za a gurfanar da shi a kotu a ranar Litinin.

Advertisement

Trump ya wallafa hoton ɗan bindigar, wanda aka bayyana sunansa da Tomas Allen, mai shekara 31, wanda malamin makaranta ne da ke aikin wucin gadi a Otel din Washington Hilton, inda abin ya faru.

Karo na biyu ke nan da ake kai harin bindiga a tarukan da Trump ke halartar a cikin ’yan shekaru.

Advertisement

Idan ba a manta ba, a watan Yuli shekarar 2024, a wurin taron yaƙin neman zaɓen Trump siyasa a Pennsylvania, Trump ya tsallake rijiya da baya, bayan wani ɗan bindiga ya harbe shi, har ya yi masa ƙwarzane a kunne.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending